NDDC: Mun fitar da sunayen wadanda suke karbar kudin kwangiloli ne don kunyatasu

NDDC: Mun fitar da sunayen wadanda suke karbar kudin kwangiloli ne don kunyatasu

Hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta (NDDC) ta ce jerin sunaye wadanda Godswill Akpabio, ministan harkokin Neja Delta ya fitar na wadanda ya bai wa kwangila sahihi ne.

Akpabio ya bayyana wasu 'yan majalisar tarayya da tsoffin gwamnoni a matsayin wadanda suka karba kwangila daga hukumar.

Peter Nwaoboshi, shugaban kwamitin kula da NDDC; Matthew Urhoghide, shugaban kwamitin asusun gwamnati; da Orji Uzor Kalu, bulaliyar majalisa, suna daga cikin 'yan majalisar da suka mora daga kwangilolin.

James Ibori da Emmanuel Uduaghan, tsoffin gwamnonin jihar Delta, suna daga cikin wadanda aka bayyana.

Dukkansu sun musanta karbar kwangilolin inda suka zarga Akpabio da kokarin bata musu suna.

Amma a wata takarda da Charles Odili ya fitar a ranar Talata, ya ce an samo wadannan sunayen ne daga takardu 8,000 da aka mika don duba yadda aka kashe kudin hukumar.

"Kwamitin rikon kwarya na hukumar na nan tsaye a kan wannan jerin sunayen da ya fitar wanda aka samo daga takardun da hukumar ke da ita," yace.

NDDC: Mun fitar da sunayen wadanda suke karbar kudin kwangiloli ne don kunyatasu
NDDC: Mun fitar da sunayen wadanda suke karbar kudin kwangiloli ne don kunyatasu. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Rashawa: Buhari ya bayyana yadda wasu makusantansa suka ci amanarsa

"Jerin sunayen ba daga Akpabio suke ba, daga NDDC suke kuma a halin yanzu bangaren binciken yadda aka kashe kudin a hukumar na da takardu 8,000.

"Akwai wasu fitattun 'yan Neja Delta da sunayensu ya bayyana, amma kada hankalinsu ya tashi don an san mutanen da suka yi amfani da sunayensu don karbar kwangiloli.

"Amfanin wannan jerin sunayen shine fallasa shugabannin kwamitin majalisar tarayyar wadanda suke karbar kwangila daga hukumar ba tare da sun aiwatar ba," ya kara da cewa.

A watan Oktoban 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci bayani dalla-dalla na yadda aka kashe kundin hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta tun daga 2001 zuwa 2019.

Ana zargin hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta da handamar wasu makuden kudade wadanda aka ware don amfanar yankin.

Amma kuma, ministan kula da cigaban yankin, Godswill Akpabio ya fasa kwai inda yace ba kwangilolin da suka bada kuma ba a aiwatar ba duk suna hannun wasu daga cikin 'yan majalisar ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel