Rashin tsaro: Za mu dawo da yardar da 'yan Najeriya suka yi mana - Buhari

Rashin tsaro: Za mu dawo da yardar da 'yan Najeriya suka yi mana - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu ya ce 'yan Najeriya sun sare a kan fannin tsaron kasar nan.

Babban mai bada shawara a kan tsaron kasa, Manjo Janar Babagana Monguno ya bayyana hakan a ranar Talata.

Yayi jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan ganawarsu da shugabannin tsaro a gidan gwamnati, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Sauran wadanda suka samu halartar taron sun hada da Osinbajo, shugabannin tsaro, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da sauransu.

Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya dawo da wannan yardar.

Kamar yadda yace, shugaban kasar ya bukaci shugabannin tsaron da su sauya salon aikinsu don gujewa ci gaban barna a kasar nan.

Monguno ya ce a wannan taron, an tattauna a kan muhimmanci abubuwa biyu da suka hada da safarar miyagun kwayoyin tare da tsarin yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Tsaro: Za mu dawo da yardar da 'yan Najeriya suka yi mana - Buhari. Hoto daga The Cable
Tsaro: Za mu dawo da yardar da 'yan Najeriya suka yi mana - Buhari
Asali: UGC

KU KARANTA: Kyawawan hotunan 'ya'ya mata na Bashir El-Rufai, dan uwan gwamnan Kaduna

NSA na shugaban kasar ya ce, kokarin da suke bai haifar da abinda ake so ba amma matsalar da ake samu na tsarin ayyuka ne wanda ministan tsaro, Bashir Magashi na aiki a kan wani abu wanda akwai yuwuwar ya bada sabuwar akala ga cibiyoyin tsaro.

Ya ce amfani da miyagun kwayoyi a fadin kasar nan yana da alaka mai karfi da rashin tsaron kasar nan. Ya ce rikici da sauran matsalolin tsaro na aukuwa ne sakamakon ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Ya ce Buhari ya jaddada cewa 'yan Najeriya sun riga sun cire rai a fannin tsaron kasar nan amma a shirye yake da ya dawo da wannan yardar.

A wani labari na daban, hukumar bunkasa yankin Niger Delta NDDC ta gayyaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sa albarka ta hanyar bude aikin titi mai kilomita 29 daga Ogbia zuwa Nembe a jihar Bayelsa.

Hukumar, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, mai taken 'NDDC ta gayyaci shugaba Buhari bude aiki', ta ce aikin, wanda ya ratsa garuruwa 14 zai ci kudi har naira biliyan 24.

Sanarwar dauke da sa hannun daraktan harkokin huldodi, Charles Odili, a Abuja, ta ce titin an ginashi ne bisa hadin guiwar hukumar da kamfanin mai na Shell.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel