Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 304 sun kamu da COVID-19 a Nigeria, Abuja na da 90

Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 304 sun kamu da COVID-19 a Nigeria, Abuja na da 90

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu daga shafin hukumar dakile yaduwar cutuka ta Nigeria (NCDC) a Twitter @NCDCGov na nuni da cewa sabbin mutane 304 sun kamu da cutar nan mai hatsari ta COVID-19 a Nigeria.

Kamar yadda kuka saba, Legit.ng Hausa na kawo maku kididdigar mutane da cutar ta kama a kowacce jiha, kamar yadda hukumar NCDC ta ke wallafawa a daren kowacce rana.

Ga jadawalinsabbin mutanen da cutar da kama da jihohinsu:

FCT-90

Lagos-59

Ondo-39

Taraba-18

Rivers-17

Borno-15

Adamawa-12

Oyo-11

Delta-9

Edo-6

Bauchi-4

Kwara-4

Ogun-4

Osun-4

Bayelsa-3

Plateau-3

Niger-3

Nasarawa-2

Kano-1

Mutane 44,433 ke dauke da cutar a halin yanzu, yayin da aka sallami mutane 31,851 daga asibiti bayan warkewarsu daga cutar, sai kuma mutane 910 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel