Ana wata ga wata: Yan kasuwa za su kara farashin litar mai zuwa N150
- Yan kasuwa na ci gaba da matsin lamva kan a kara kudin man fetur zuwa N150 akan kowacce lita daga watan Agusta
- Hakan ya biyo bayan karuwar farashin danyen mai a kasuwar mai ta duniya
- A watan da ya gabata ne hukumar PPRA ta sanar da karin kudin man fetur daga N140.80 zuwa N143.80 akan kowacce lita
Biyo bayan karuwar farashin danyen mai, 'yan kasuwa na ci gaba da matsin lamva kan a kara kudin man fetur zuwa N150 akan kowacce lita daga watan Agusta.
Hukumar da ke kayyade farashin man fetur ta kasa (PPRA) a watan da ya gabata ta sanar da karin kudin man daga N140.80 zuwa N143.80 akan kowacce lita.
Wannan shine karo na farko da hukumar ta amince da karin farashin man, tun bayan da aka cire tallafin man fetur a kasar.
Kafin daga farashin man a ranar 1 ga watan Yuli, a ranar 1 ga watan Yuli, hukumar ta amince da sayar da litar mai daga N121.50 zuwa N123.50.
KARANTA WANNAN: NDDC ta gayyaci Buhari ya bude wani babban aikinta da yaci N24bn a Bayelsa

Asali: Facebook
A wani labarin kuwa, wata majiya mai tushe ta shaidawa jaridar The Nation cewa 'yan kasuwa na yunkurin kara fashin man fetur sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.
Gangar mai da ake sayarwa akan $43.24 a watan Yuli yanzu ta dawo ana sayar da ita akan $44.03.
Jaridar ta ruwaito cewa, "a yanzu ana cikin wani taro domin cimma matsaya ta sabon farashin da za a rinka sayar da man fetur daga watan Agusta.
"Yan kasuwa na bukatar PPRA da ta amince a sayar da man akan N150 kowacce lita daya saboda kudin danyen mai ya tashi kuma an janye tallafin mai a kasar."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng