Buɗe Makarantu: NUC ta fara tantance jami'o'in Najeriya

Buɗe Makarantu: NUC ta fara tantance jami'o'in Najeriya

Hukumar da ke sa ido kan jami’o’i a Najeriya NUC, ta ce ta fara tattaro bayanai daga jami’o’i a fadin kasar domin tabbatar da shirinsu na komawa bakin aiki.

Hukumar ta ce ana ci gaba da fafutikar kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ke faman yi tun tsawon watanni da dama da suka gabata kawo yanzu.

NUC ta ce yajin aikin da kungiyar ASUU ke yi yana baranza tare da taka rawa wajen kawo tsaiko a harkokin karatu a jami’o’in kasar.

Babban sakataren hukumar NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, shi ne ya sanar da hakan a wani taro na manema labarai dangane da gudunmuwar da jami’o’in kasar ke bayar wa wajen yaki da annobar korona.

Hukumar NUC
Hoto daga jaridar Premium Times
Hukumar NUC Hoto daga jaridar Premium Times
Asali: Twitter

Ana iya tuna cewa tun a watan Maris gwamnatin tarayya ta ba da umarnin rufe kafatanin makarantu manya da kanana a sakamakon barkewar annobar korona.

A cewar Farfesa Rasheed wanda mataimakinsa Suleiman Yusuf ya wakilta a taron wanda aka gudanar a ranar Talata cikin birnin Abuja, NUC na ci gaba da fadi-tashi tare da jami’o’i da tattaunawa a kan matakan da za a shimfida gabanin komawa aiki.

KARANTA KUMA: Zan kammala dukkan ayyuka na a 2022 - Masari

Ya ce jami’o’in da bas a karkashin jagorancin kungiyar ASUU za su iya komawa bakin aiki da zarar dukkan matakan da aka shata sun tabbata kuma an kiyaye su.

A ranar 9 ga watan Maris ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki na gargadi, inda kuma a ranar 23 ga watan Maris ta zarce da na sai mama ta gani.

ASUU ta shiga yajin aikin ne a sakamakon rashin biyan albashin wasu daga cikin mambobinta da suka ki karbar sabon tsarin biyan albashi na bai daya wato IPPIS da gwamnatin tarayya ta kawo domin dukkan ma’aikatan gwamnati.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel