An dakatar da dan majalisar jihar Ondo saboda zagin kakakin majalisa

An dakatar da dan majalisar jihar Ondo saboda zagin kakakin majalisa

An dakatar da dan majalisar jihar Ondo, Leonard Tomide Akinribido, da aka zaba a karkashin jam'iyyar Labour kamar yadda The Nation ta ruwaito.

An dakatar da Akinribido, mai wakiltan mazabar Ondo ta Yamma 1, saboda saba dokokin majalisa da zagin Kakakin Majalisa, Bamidele Oleyelogun a zauren majalisar da kuma a dandalin sada zumunta ta WhatsApp.

An umurci Akinribido ya ajiye dukkan takardun aiki da ke hannunsa sannan an hana shi zuwa harabar majalisa tsawon waadin dakatar da shi da aka yi.

An dakatar da dan majalisar jiha saboda zagin kakakin majalisa
An dakatar da dan majalisar jiha saboda zagin kakakin majalisa. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Jirgin UN ya yi hatsari a Mali (Hoto)

Makonni uku da suka gabata, Majalisar da dakatar da wasu 'yan majalisa uku saboda saba dokokin aiki.

Wadanda aka dakatar a bayan sun hada da mataimakin Kakakin Majalisa, Hon. Adewale Williams da Hon. Favour Tomomewo.

Dan majalisar jihar Ondo da aka dakatar, Leonard Tomide Akinribido ya yi martani a kan matakin da majalisar ta dauka a kansa.

Ya ce an dakatar da shi ne saboda ya ki goyon bayan yunkurin da aka yi na tsige mataimakin gwamnan jihar, Hon Agboola Ajayi.

A wata takaitaciiyar hira da ya yi da manema labarai, Akinribido ya ce siyasa ce ta saka aka dakatar da shi.

Ya bayyana dakatarwar a matsayin bita da kulli kuma ya musanta cewa ya yi wa kakakin majalisar ashararinci kamar yadda ake zarginsa.

Akinribido ya ce masu neman tsige shi sun kara bayar da himma ne yayin da suka gano mataimakin gwamnan yana shirin koma wa Zenith Labour Party.

Ku saurari karin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel