Jihar Taraba ce kadai babu wanda ya mutu sakamakon cutar Coronavirus

Jihar Taraba ce kadai babu wanda ya mutu sakamakon cutar Coronavirus

Duk da yadda adadin masu kamuwa da cutar Korona ke karuwa a Najeriya da mutane 896 suka mutu, jihar Taraba ce jiha daya tilo a kasar da ba'a samu wanda ya mutu ba, Daily Trust ta hararo.

Alkaluma daga hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC kawo ranar Litinin 3 ga Agusta, ya nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya ya kai 44,129 da mutane 20,663 sun samu waraka.

Jihar Legas ce mafi yawan adadin wadanda sukayi wafati sakamakon cutar - 192 - sai jihar Edo 87, sannan jihar Kano da Rivers masu 53 kowanne.

Kawo yanzu a jihar Taraba, mutane 54 kadai suka kamu da cutar. Yayinda aka sallami 11, 43 na jinya har yanzu amma babu wanda ya mutu.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara feshin makarantu 19,000 da za'a zana jarabawar WAEC

Jihar Taraba ce kadai babu wanda ya mutu sakamakon cutar Coronavirus
Jihar Taraba ce kadai babu wanda ya mutu sakamakon cutar Coronavirus
Asali: Twitter

Shin ya kare kenan?

A ranar 17 ga Mayu, jihar Taraba ta sallami dukkan mutane 17 da suka kamu da cutar a jihar bayan samun waraka.

Gwamna Darius Ishaku ta tabbatar da hakan ga manema labarai yayinda ya tafi yawon duba cibiyar killacewa dake sansanin NYSC a Sibre, a karamar hukumar Ardo-Kola na jihar.

Babu cibiyar gwaji

Gwamnan ya koka kan rashin cibiyar gwajin cutar a jihar, inda yayi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da cibiyar gwaji ko da guda daya.

Duk da cewa an sanya dokar hana fita domin takaita yaduwar cutar, gwamnatin ta janye dokar don zaben kananan hukumomi da ya gudana ranar 30 ga Yuni.

Komawan dalibai aji

A ranar Alhamis kuma bisa ga umurnin gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Taraba ta bukaci yan ajin karshe a makarantun sakandare su koma karatu yau, 4 ga Agusta, 2020.

Gwamnatin tayi bayanin cewa an yi haka ne domin baiwa dalibai dama karatu kafin fara zana jarabawan kammala karatun sakandare WAEC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel