Zan kammala dukkan ayyuka na a 2022 - Masari

Zan kammala dukkan ayyuka na a 2022 - Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sha alwashin kammala dukkan ayyukan da yake aiwatar wa a yanzu kafin karshen shekarar 2022.

Da yake magana yayin kaddamar da kwamitin mutum bakwai da za su sa ido wajen kammala ayyukan, Masari ya ce gwamnatinsa ba za ta sake bijiro da wani sabon aiki ba face matsananciyar bukatar hakan ta taso.

A cewarsa, rashin tsaro musamman ta'addancin 'yan daban daji da kuma annobar korona sun sanya matsin lamba kan duk albarkatun jihar.

Masari ya ce duk da wannan kalubale, zai jajirci wajen ganin gwamnatinsa ta kammala ayyuka da take aiwatar a sashen Ilimi, Noma, Lafiya da sauransu.

Gwamnan Jihar Katsina; Aminu Bello Masari
Gwamnan Jihar Katsina; Aminu Bello Masari
Asali: Facebook

Kwamitin wanda Gwamna Masari ya kaddamar da kuma Mansur Ahmed Kurfi a matsayin jagoransa, ya kunshi mambobi da aka zakulo daga ma'aikatu daban-daban masu zaman kansu.

Daga cikin nauyin da aka rataya wa kwamitin; akwai bukatar gano da kuma tattara bayanan duk ayyukan da suke gudana, tantance matsayinsu da matakin ci gaba da suke kai a yanzu.

KARANTA KUMA: Tambuwal ya saki fursunoni 17 a jihar Sakkwato

Sauran nauye-nauyen sun hadar da samar da dabarun tabbatar an kammala ayyukan ta hanyar rarraba su zuwa karami, matsakaici da na dogon zango.

Haka kuma an bukaci kwamitin ya janyo hankalin gwamnati kan tsare-tsaren da za a bi domin tabbatar da kammaluwar ayyukan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gana da majalisar tsaron tarayya tare da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, a fadar shugaban kasa dake Aso villa Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci ganawar sun hadar da shugaban dakarun tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; babban hafsan sojin sama, Air marshal Sadique Baba Abubakar; babban hafsan Sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai.

Akwai kuma babban hafsan Sojin ruwa, Ibek Etas da Sifeto Janar na yan sanda, IG Adamu Mohammed; shugaban hukumar tsaron farin kaya, Yusuf Magaji Bichi; shugaban hukumar leken asirin kasa, Ahmed Rufa'i.

Hakazalika akwai mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno; ministan shari'a, Abubakar Malami; ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi; ministan harkokin yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi; ministan harkokin cikin gida, Aregbesola.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng