Da duminsa: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da majalisar tsaron tarayya (Hotuna)

Da duminsa: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da majalisar tsaron tarayya (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka yana ganawa da majalisar tsaron tarayya tare da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, a fadar shugaban kasa dake Aso villa Abuja.

Daga cikin wadanda ke hallare a ganawar sune shugaban hukumar tsaron kasa, Janar Gabriel Olonisakin; shugaban mayakan sama, Air marshal Sadique Baba Abubakar; babban hafsan Sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, babban hafsan Sojin ruwa, Ibek Atas da Sifeto Janar na yan sanda, IG Adamu Mohammed.

Hakazalika akwai mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno,; shugaban hukumar tsaron farin kaya, Yusuf Magaji Bichi; shugaban hukumar leken asirin kasa, Ahmed Rufa'i.

Sauran sune ministan shari'a, Abubakar Malamil ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi; ministan harkokin yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi; ministan harkokin cikin gida, Aregbesola, dss.

Ganawan ya biyo bayan jawabin sakon murnar sallah da shugaban Muhammadu Buhari yayi kan tsaro.

Buhari ya ce yan Najeriya sun san gwamnatinsa ta yi iyakan kokarinta wajen shawo kan matsalan tsaro da ake fama da shi a fadin tarayya.

Yayinda yake magana da manema labaran fadar shugaban kasa bayan Sallar Idi a fadar shugaban kasa Aso Villa, shugaban kasan yace ba lokacinsa aka fara fuskantar matsalar tsaro ba.

Amma ya nuna bacin ransa kan gazawan hukumomin tsaro , inda yace ya kamata a ce sun fi hakan kokari.

Yace: "Ina son yan Najeriya su farga kan kasarsu kuma su san abinda muka gada lokacin da muka dau mulki a 2015 Boko Haram ne a Arewa maso gabas sannan barandanci a Kudu maso kudu.... Yan Najeriya sun san munyi iyakan kokarinsu."

"Abinda ke faruwa a Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya na da matukar takaici amma nayi imanin cewa Sojoji, yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su kara kokari."

Da duminsa: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da majalisar tsaron tarayya (Hotuna)
Da duminsa: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da majalisar tsaron tarayya (Hotuna)
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel