Yanzu-yanzu: Jirgin UN ya yi hatsari a Mali (Hoto)

Yanzu-yanzu: Jirgin UN ya yi hatsari a Mali (Hoto)

Wani jirgin Majalisar Ɗinkin Duniya, UN, ya kwace wa matuƙin jirgin yayin da ya ke sauka a filin tashi da saukar jirage ta Gao da ke Mali a ranar Litinin.

Mutane 11 cikin daga cikin wadanda ke jirgin sun jikkata kamar yadda Tawagar Samar da Zaman Lafiya ta UN a Mali, MINUSMA ta ruwaito.

Jirgin na UN ya yi ƙoƙarin yin saukar gaggawa ne kafin ya kauce daga titinsa ya yi hatsarin.

Kawo yanzu dai UN ba ta fayyace abinda ya yi sanadin hatsarin jirgin ba kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Jirgin UN ya yi hatsari a Mali
Jirgin UN ya yi hatsari a Mali. Hoto daga @HaidaraFigo
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ba zan iya tuna adadin mutanen da na kashe ba - Tsohon ɗan Boko Haram

"Wani jirgin MINUSMA daga Bamako dauke da mutum 11 (fasinjoji hudu, ma'aikatan UN da ma'aikatan jirgin bakwai) sun yi hatsari yayin sauka a filin tashi da saukan jirage ta Gao," in ji sanarwar.

"Za a fara bincike domin gano sababin afkuwar hatsarin nan ba da dadewa ba."

A halin yanzu dai akwai wasu masu tayar da ƙayan baya a ƙasar Mali da ke ƙoƙarin hambarar da Shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

Keita ya yi shekaru biyu cikin biyar na wa'adin mulkinsa kawo yanzu.

Hukumar hadin kan kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, ta nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin shugaban tawagar warware matsalar siyasar kasar Mali.

A baya bayan nan Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar ta Mali bayan tawagar da Jonathan ta yi masa bayani a kan abinda ke faruwa a Mali.

Sauran shugabannin kasashen Afirka ta Yamma sun hadu da Buhari a birnin Bamako inda suka tattauna kan hanyoyin da za su bi don shawo kan matsalar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel