Gwamnoni za su gana da shugaban kasa game da rashin tsaro

Gwamnoni za su gana da shugaban kasa game da rashin tsaro

A ranar Litinin da ta gabata ne gwamnonin jihohi 36 na fadin tarayya, suka bayyana damuwa dangane da yadda lamari na rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar.

Sanadiyar hakan ne ya sanya gwamnonin karkashin kungiyarsu ta NGF, suka yanke shawarar garzaya wa har fadar shugaban kasa domin gudanar da zama na musamman da shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnonin bayan zaman kwamitinsu na tsaro, sun yanke shawarar kai wa shugaban kasa Buhari koken al'ummarsu dangane da hali na rashin tsaro da ya ke kara tsananta.

Gwamnonin yayin bayyana damuwa dangane da harin da ake zargi 'yan Boko Haram sun kai wa ayarin motocin gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, sun kuma nuna bacin rai a kan tabarbarewar tsaro duk da kokarin gwamnatin tarayya.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya
Kungiyar Gwamnonin Najeriya
Asali: Facebook

Sai dai sun yi farin ciki a yayin da gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya ba tare da ko kwarzane ba yayin da harin ya auku.

Haka kuma gwamnonin sun bayyana damuwa kan yadda wasu jami'ai biyu na rundunar hadin gwiwa da kuma jami'in dan sanda daya suka raunata yayin mayar da martanin harin.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa, gwamnonin sun cimma matsayar hakan ne cikin wata wasikar jaje da suka aikewa gwamna Zulum mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

Fayemi ya ce kwamitin tsaro na kungiyar gwamnonin ta shirya gudanar da wani zama na musamman a yau Talata, inda daga nan za ta zartar da shirin ganawa da shugaba Buhari da kuma hafsoshin tsaro.

KARANTA KUMA: Za a buɗe makarantun Kano a ranar 10 ga watan Agusta

A ranar Larabar makon jiya ne aka kaiwa tawagar gwamna Zulum hari yayin da ya je kan hanyarsa ta zuwa garin Baga da ke karkashin karamar hukumar Kukawa a jihar Borno.

Sai dai gwamnan ya dora alhakin harin da aka kaiwa tawagarsa ranar Laraba ta makon jiya a kan sojojin Najeriya.

Da ya ke magana da kwamandan rundunar soji jim kadan bayan kai wa ayarinsa hari, Gwamna Zulum ya nuna bacin ransa a kan yadda sojoji su ka gaza kwace garin Baga duk da yawan rundunoninsu da ke jibge a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel