Har yanzu hankulan mu ba su kwanta ba game da bude makarantu – FG

Har yanzu hankulan mu ba su kwanta ba game da bude makarantu – FG

A yayin da wasu daga cikin daliban makarantun frimare da sakandare ke shirin komawa makarantu a yau, SSG kuma shugaban kwamitin yaki da korona na shugaban kasa, Boss Mustapha ya ce har yanzu hankalinsa bai kwanta ba game da lamarin.

A cewarsa, yana damuwa ne "domin makarantu na daya daga cikin hanyoyin da cutar za ta iya yaduwa cikin alumma idan ba dauki matakan da suka dace ba kuma an bi dokoki."

Da ya ke magana ranar Juma'a a Abuja yayin jawabin na PTF, Mustaha ya roki masu ruwa da tsaki a harkar su tabbatar sun bi dokokin da aka saka domin dakile yaduwar cutar.

Har yanzu hankulan mu ba su kwanta ba game da bude makarantu – FG
Boss Mustapha. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana cewa PTF din tana dab da kammala tattaunawa da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC kan hanyoyin da za a bi domin gudanar da zabe a jihohin Edo da Ondo.

DUBA WANNAN: Ba zan iya tuna adadin mutanen da na kashe ba - Tsohon ɗan Boko Haram

Ya gargadi shugabannin jam'iyyu, yan takara, mambobin jamiiya da magoya baya su kula da cewa COVID-19 na nan yana yaduwa a lokacin da suke harkokin zabe da kamfe.

Ya ce, "Sai muna da rai za mu mori romon demokradiyya."

Ya kara da cewa an fara sanya idanu a wasu kananan hukumomi da aka lura cutar tana yaduwa a kasar. "A halin yanzu ana sa ido a kananan hukumomi da cutar ta yi musu katutu."

Ya ce kwamitin ta PTF za ta mika wa shugaban kasa rahoton ta ta 6 "kuma da amincewarsa PTF din za ta gabatarwa yan Najeriya matakin da za a dauka a ranar Alhamis mai zuwa."

Mustapha ya kuma bayyana cewa a yunkurin da ECOWAS ke yi don yaki da Covid 19 a Afirka ta Yamma, Buhari ya bawa kasar Sao Tome and Principe tallafin kayan asibiti da kudinsa ya kai Naira miliyan 67.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164