Ku kiyayi Kogi, Gwamna Bello ya gargadi masu garkuwa da mutane

Ku kiyayi Kogi, Gwamna Bello ya gargadi masu garkuwa da mutane

- Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya gargadi masu garkuwa da mutane da sauran ɓata gari su kiyayi jiharsa

- Gwamnan ya ce za suyi amfani da kuruwar iyaye da kakanninsu wurin magance duk wata barazanar tsaro a jihar

- Gwamna Bello ya yi wannan gargadin ne wurin taron naɗin sarautar kwamishinan ma'adinai Injiniya Abubakar Bashir Gegu

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya gargadi masu garkuwa da mutane, ɓarayin shanu da ƴan bindiga su kiyayi jiharsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan gargadin ne yayin naɗin sarautar kwamishinan ma'adinai, Injiniya Abubakar Bashir Gegu wasu mutane 64 da Onyiwo na Gegu-Beki, Mohammed Abbas ya yi a ranar Lahadi.

Ku kiyayi Kogi, Gwamna Bello ya gargadi masu garkuwa da mutane
Ku kiyayi Kogi, Gwamna Bello ya gargadi masu garkuwa da mutane.
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ba zan iya tuna adadin mutanen da na kashe ba - Tsohon ɗan Boko Haram

Ya ce fushin iyaye da kakannin ƴan kabilar Egbira zai faɗa a kan duk wani da ya nemi ya fara aikata laifuka kamar satar shanu da garkuwa da mutane da sauransu.

Ya ce ƴan kabilar Egbira da suka fito daga Kwararafa mutane ne masu yawa, ƙarfi, maraba da baƙi, aiki tukuru da juriya.

Ya ce akwai ɗimbin ma'adinan ƙasa a Gegu-Beki kuma ƙasar ta dace da noma kana akwai kifaye da wasu dabbobin ruwa a rafin da ke garin.

"Za mu yi amfani da ƙarfin iyayen mu da ƙanƙanin mu don magance duk wani barazana kuma muna da karfafan maza da mata da a shirye su ke su magance duk wata barazanar tsaro," in ji shi.

A jawabinsa, Onyiwo na Gegu-Beki, Alhaji Muhammad Alhassan Abba, ya yabawa gwamnan bisa ƙokarinsa wurin samar da tsaro a jihar.

A wani labarin, shugaban hafsin sojojin saman Najeriya, Air Vice Marshall Sadique Abubakar ya ce za a samar da jirage marasa matuƙa, UAVs, domin kawo karshen ayyukan ƴan bindiga a Katsina da Zamfara.

Shugaban sojin ya bayyana hakan ne yayin wata walima da aka shirya don bikin Babbar Sallah da sojoji a jihohin yankin arewa maso yamma kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina a jawabinsa ya yi iƙirarin cewa a halin yanzu ƴan sanda 30 ne kacal ke bawa ƙauyuka 100 tsaro a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel