Gwamnatin tarayya ta fara feshin makarantu 19,000 da za'a zana jarabawar WAEC

Gwamnatin tarayya ta fara feshin makarantu 19,000 da za'a zana jarabawar WAEC

Ma'aikatar mahallin tarayya tare da hadin kan ma'aikatar ilimi ta kaddamar da shirin feshi a makarantu 19,000 da za'a zana jarabar karshe a makarantun sakandare watau SSCE.

Ministan mahalli, Dr Mahmoud Abubakar, yayinda yake hira da manema labarai a Kaduna ya ce ma'aikatun sun shirya tsarin da zai kare lafiyar dalibai da malamansu.

Yayinda yake tabbatarwa iyaye cewa yaransu zasu kasance cikin lafiya, ya bukaci su tabbatar da cewa yaran na sanye da rigar fuska lokacin jarabawa.

"An fara da makarantun gwamnatin tarayya FGC, sannan wasu makarantun da za'a gudanar da jarabawan karshe a matakin sakandare, kimanin su 19,000."

"Wasu ma'aikatanmu zasu rika lura da yadda abubuwa ke gudana a cibiyoyin jarabawar."

"Za'a rika feshin dakunan jarabawa bayan kowani zaman jarabawa da aka yi. Game da haka, Yanzu zamuyi amfani da sinadarin kashe kwayoyin cuta maras illa ga dan Adam da mahalli." Ministan ya laburta

Gwamnatin tarayya ta fara feshin makarantu 19,000 da za'a zana jarabawar WAEC
Gwamnatin tarayya ta fara feshin makarantu 19,000 da za'a zana jarabawar WAEC
Asali: UGC

KU KARANTA: Mun kashe sama da milyan 500 wajen ciyar da yan makaranta lokacin dokar kulle - Ministar Walwala

Mun kawo muku rahoton cewa yau Talata za a buɗe duk makarantun sakandire na gwamnatin tarayya 104 kamar yadda karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya ba da sanarwa.

Ministan ya ba da sanarwar hakan ne a ranar Litinin, 3 ga watan Agusta, yayin da ya kammala tattaunawa da kwamishinonin ilimi na jihohi 36 da ke fadin tarayya da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun ma'aikatar ilimi ta tarayya, Ben Goong ya sanya wa hannu, ya yabi shugabannin makarantun dangane da tabbatar duk wani shiri na komawar ɗalibai a gobe Talata.

Tun a ranar 26 ga watan Maris ne Gwamnatin Tarayya ta rufe duk makarantun kasa, matakin da ya shafi makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel