Mun kashe sama da milyan 500 wajen ciyar da yan makaranta lokacin dokar kulle - Ministar Walwala
Gwamnatin tarayya ta kashe milyan N523.3 wajen ciyar da daliban makarantan firamare a gidajensu lokacin dokar zama a gida sakamakon cutar Coronavirus.
Ministar Walwala, tattalin annoba, da jinkai, Sadiya Farouq, ta sanar da haka ne a zaman hira da manema labaran kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID19 a ranar Litinin a Abuja, Vanguard ta ruwaito.
Sadiya ta bayyana hakan ne domin watsi da jita-jita da raye-rayen da akeyi kan adadin kudin da aka kashe wajen ciyar da yaran lokacin dokar kulle.
Ta ce an sauya fasalin shirin ne kuma aka aiwatar a jihohi uku bisa umurnin da shugaban kasa ya bada ranar 29 ga Maris.
"Yana da muhimmanci yanzu mu saki bayanin da zai birne karerayin da ake yi a waje."
"Wannan shiri ba tsarin Ma'aikatar kadai bane, umurnin shugaban kasa muka bi."
"Ma'aikatar ta yi shawara da gwamnatocin jihohi ta kungiyar gwamnonin Najeriya kuma aka yanke shawaran kan cewa basu danyen abinci ne hanya mafi saukin ciyar da daliban cikin dokar zaman gida."
"Masu ruwa da tsakin sun yanke cewa a fara da Abuja, Legas da Ogun." Ministar tace.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Allah ya yiwa babban Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass rasuwa, Buhari ya aika sakon ta'aziyya
A cewar Hajiya Sadiya, an yi ittifakin cewa rabon kowani gida daya zai kasance N4,200 a wata. An yanke hakan ne bisa alkaluma daga bankin CBN da cibiyar lissafin kasa NBS.
A cewar NBS da CBN, kowani gida a Najeriya na da kimanin mutane 5.6, yara uku zuwa hudu.
"Saboda haka mukayi kiyasin cewa kowani gida akwai yara uku. Farashin abincin dalibi kowani rana daya zai kasance N70. Idan ka hada na kwanaki 20 zai zama N1,7000 a wata."
"Saboda hakan na yara uku zai zama N4,200 a wata. Haka muka yi kiyasin farashin kaso kowani gida." Sadiya tace
Ta ce ma'aikatar ta gayyaci ma'aikatun gwamnati irinsu EFCC, CCB, ICPC, DSS da wasu kungiyoyi masu zaman kansu domin duba yadda rabon ke gudana.
"A birnin tarayya gidaje 29,609 aka rabawa, a Legas gidaje 37,589 suka samu kuma a gidaje 60,391 a Ogun. Jimillan gidaje 124,589 suka samu tsakanin 14 ga Mayu da 6 ga Yuli."
"Idan gidajen 124,589 suka samu kaso da akayi kiyasi a N4,200, adadin zai zama N523, 273, 800."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng