Sabbin mutum 288 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 288 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:44 na daren ranar Litinin 4 ga Augustan shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 288 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Asali: Facebook
Lagos-88
Kwara-33
Osun-27
FCT-25
Enugu-25
Abia-20
Kaduna-17
DUBA WANNAN: Jirgin sama makare da hodar-Iblis ya yi hatsari lokacin da ya ke kokarin tashi
Plateau-13
Rivers-13
Delta-10
Gombe-8
Ogun-4
Oyo-3
Katsina-1
Bauchi-1
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Litinin 4 ga Augustan shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 44,129 .
An sallami mutum 20,663 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 896.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng