Masu cutar korona a Najeriya sun kai 43,841 - NCDC
- A yanzu cutar korona ta bulla a duk jihohi 36 na Najeriya da kuma babban birnin kasar na Tarayya
- Jihar Legas ce ke jan ragama inda ta harbi mutum 15,267, mutum 2,160 suka warke sai kuma mutum 192 da suka riga mu gidan gaskiya
- A halin yanzu cutar ta harbi mutum 43,841, sai kuma mutum 20,308 da suka samu waraka, yayin da mutum 888 suka riga mu gidan gaskiya
Ya zuwa yanzu dai an samu bullar cutar korona a duk jihohi 36 na Najeriya da kuma birnin tarayya kamar yadda kididdigar hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC ta tabbatar.
Tabbas mahukuntan lafiya na ci gaba fadi-tashi ba dare ba rana domin dakile yaduwar cutar korona a Najeriya, sai dai fa lamarin ya ci tura domin kuwa cutar na ci gaba da bazuwa tamkar wutar daji.
Taskar bayanai ta NCDC a ranar Lahadi, 2 ga watan Agustan 2020, ta ce cutar korona ta harbi mutane 43,841 a duk fadin kasar.

Asali: Twitter
Haka kuma alkaluman sun nuna cewa an sallami mutum 20,308 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan da suka warke.
Jadawalin NCDC ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu dai cutar korona ta hallaka mutum 888 a fadin kasar.
KARANTA KUMA: Ku kare kanku daga harin makiyaya da na 'yan daban daji - Kaigama ya shawarci 'yan Najeriya
Da misalin karfe 11.26 na ranar Lahadi da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 304 da cutar ta harba a fadin Najeriya.
Sabbin mutane 304 da cutar ta harba cikin jihohin 15 sun kasance kamar haka:
Legas (81), Abuja (39), Abia (31), Kaduna (24), Ribas (23), Filato (16), Cross River (13), Ebonyi (12), Ondo (12) Ekiti (11), Edo (11), Benuwe (10), Nasarawa (10), Ogun (6), Gombe (5)
Har ila yau jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, sai kuma birnin Abuja a mataki na biyu yayin da jihar Oyo ta biyo bayansu a mataki na uku.
Legas - 15,267
Abuja - 3,972
Oyo - 2,768
Edo - 2,311
Rivers - 1,829
Kano - 1,597
Delta - 1,510
Kaduna - 1,481
Ogun - 1,403
Filato - 1,227
Ondo - 1,204
Enugu- 821
Ebonyi - 808
Kwara - 753
Katsina - 745
Borno - 613
Gombe - 612
Abia - 582
Bauchi - 560
Osun - 553
Imo - 469
Benue - 356
Nasarawa - 339
Bayelsa - 339
Jigawa - 322
Neja - 223
Akwa Ibom - 221
Adamawa - 164
Sokoto - 154
Ekiti - 152
Anambra - 135
Kebbi - 90
Zamfara - 77
Yobe - 67
Cross River - 58
Taraba - 54
Kogi - 5
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng