Kyawawan hotunan sallah na IBB tare da 'ya'ya da jikokinsa

Kyawawan hotunan sallah na IBB tare da 'ya'ya da jikokinsa

- Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi babbar sallah ta shekarar 2020 tare da iyalansu makusanta

- Hotunan yadda suka sha shagalin sallah babbar ya fada yanar gizo ne ta shafin daya daga cikin diyarsa ta Instagram

- A ranar Juma'a, 31 ga watan Yulin 2020, an ga IBB zagaye da 'ya'yansa da jikokinsa inda suke shagalin bikin babbar sallah

Daya daga cikin shugabannin Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, wanda aka fi sani da IBB, ya yi shagalin bikin babbar sallarsa tare da iyalansu makusanta da suka hada da 'ya'ya da jikokinsa.

Babu shakka iyalan sun ji dadin bikin babbar sallar bana tare da tsohon shugaban mulkin sojin.

An ga tsohon shugaban kasar zagaye da iyalansa cike da kauna. Uku daga cikin manyan 'ya'yansa na cikin hoton wanda ke nuna cewa tare suka yi bikin sallah a shekarar 2020.

Hakazalika, a tare da kakan an ga jikokinsa uku wadanda suka je har gida don taya murnar babbar ranar.

A wani labari na daban, IBB ya yi martani a kan rahoton da ake yadawa wanda ke ikirarin cewa yana neman matar aure.

A yayin da aka tambayesa a wata tattaunawa da aka yi da shi idan da gaske ne yana neman matar aure, tsohon shugaban kasar ya ce: "hakan kafafen yada labarai ke so. Mutane da dama suna tambayata gaskiyar lamarin."

Tun bayan rasuwar Maryam Babangida a 2009, tsohon shugaban kasar bai sake yin aure ba sai dai zama da yake yi da 'ya'yansa.

"Ina da 'ya'ya masu kula da ni da kuma fahimta. Suna kokarin rufe gibin da mahaifiyarsu ta bari," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel