Ba zan yi shiru ba, akwai wadanda basu son rikicin Boko Haram ta kare - Zulum

Ba zan yi shiru ba, akwai wadanda basu son rikicin Boko Haram ta kare - Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa akwai masu yiwa yaki da rikicin Boko Haram a Arewa maso gabas zagon kasa kuma ya kamata shugaban kasa ya san gaskiya.

Zulum ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin gwamnonin jam'iyyar APC karkashin jagoranicn gwamnan Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu.

Gwamnonin sun kawo masa ziyarar jaje bisa harin da aka kai masa a garin Baga, karamar hukumar Kukawa, ranar Laraba, 29 ga Yuli, 2020.

Yace: "Bari in sake jaddada matsayata da nayi a baya kan yaki da ta'addanci a Borno, ina mai jaddadawa kuma ko shakka babu, ba za'a iya hada rikicin a 2011 - 2015 da 2015 zuwa yanzu ba."

"Shugaban kasa ya yi kokari, amma abu mai muhimmanci shine, yana da kyau a fadi abinda ya dace. Akwai masu zagon kasa da basu son rikicin ta'addancin nan ya kare. Ya kamata shugaban kasa ya san wannan abin mai muhimmanci."

"Yayinda ya zo Maiduguri watanni biyu da suka gabata, na fadi haka saboda tsakanin 2011 da 2015, kimanin kananan hukumomi 22 na karkashin yan ta'adda."

"Daga cikin manyan hanyoyin shiga Maiduguri hudu, guda daya kawai ke bude. Amma yanzu an samu canji. Duk da haka, akwai abu guda daya da ya kamata mu mayar da hankali, shin meyasa yakin yaki karewa?"

"Ina jaddada cewa akwai zagon kasa a lamarin nan, saboda haka, ya kamata shugaban kasa ya duba matsalar tsaron yankin nan don kawo karshenshi."

Ba zan yi shiru ba, akwai wadanda basu son rikicin Boko Haram ta kare - Zulum
Ba zan yi shiru ba, akwai wadanda basu son rikicin Boko Haram ta kare - Zulum
Asali: Facebook

A nasa bangaren, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, ya tabbatarwa gwamna Zulum cewa suna bayansa.

"Mun zo Borno yau ne a madadin takwarorinmu don taya abokinmu, Gwamna Babagana Umara Zulum murnar Sallah. Na biyu kuma mu jajanta masa bisa abinda ya faru a Baga kwanakin da suka gabata."

"Allah ya cigaba kareka da dukkan al'ummar jihar Borno, kuma Allah ya taimaka mana wajen yakan makiyan ciki da waje." Gwamna Bagudu yace.

A bangare guda, Gwamna Zulum ya bayyana takaicinsa kan yadda adadin masu zama a sansanin gudun hijra ke tashi, ya ce akwai bukatar mutane su koma gidajensu tun da a samu zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng