Dalilin da yasa Najeriya ke karbo bashi daga China - Ameachi

Dalilin da yasa Najeriya ke karbo bashi daga China - Ameachi

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a ranar Juma'a ya ce Najeriya na karbar bashi daga China ne saboda ya fi sauki ta fanin kuɗin ruwa, wa'adin biya da hukuncin saɓa lokacin biya idan an kwatanta da sauran ƙasashen Yamma.

A hirar da aka yi da ministan a gidan talabijin na AIT, ya ce idan Najeriya ta dena karbar bashi hakan na nufin ayyukan gine gine da gwamnatin tarayya ke yi za su tsaya kamar yadda The Punch ta ruwaito

Dalilin da yasa Najeriya ke karbo bashi daga China - Ameachi
Rotimi Ameachi. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

Ya ce, "Mutane na tambaya ko Najeriya za ta iya biyan basukan da muke ci. Za mu biya. An baka bashi na tsawon shekaru 20 a kan ruwa na 2.8%. Wacce ƙasa za ta baka irin wannan garaɓasar?

"Na kuma bayyana cewa ƴan kwangilan ake biya wannan kuɗin kai tsaye da zarar mun saka hannu cewa sun yi aikin. Abinda ke da muhimmanci shine ana gudanar da ayyukan.

"Idan aka kwatanta da basusukan da muke karɓowa daga ƙasashen Yamma, wannan a kan 2.8 na tsawon shekaru 20. Mai za sa ba za mu biya ba?".

Ya ce idan da gwamnatocin baya sun yi ayyukan gine gine da batun ciwo bashin ma bai taso ba a yanzu.

"Ina ganin ya kamata Majalisar Tarayya da ƴan Najeriya su yarda cewa muna samun cigaba ta fanin gine gine.

"Idan muka dena karbo bashin, toh ayyukan za su tsaya cak domin ba mu da kudi. Kafin mu hau mulki duk an bannatar da kuɗin. Babu kudi."

Ministan ya kuma yi karin haske kan iƙirarin wasu keyi na cewa Najeriya za ta sayar wa China da ƴancin ta inda ya ce hakan ba gaskiya bane.

Ya ce wannan sashin kwangilar kawai yana nufin cewa Najeriya za ta biya bashin da ta ƙarba ne amma ba wai kasar za ta rasa ƴancin ta bane.

Majalisar Wakilai ne a ranar Talata ta yi tsokaci a kan yarjejeniyar karbo bashin da Gwamnatin Tarayya za ta yi daga ƙasar China inda ta ce ya kamata a sake duba batun.

Ameachi ya ce, "Babu ƙasar da za ta sayar da ƴancin ta. Sashin ya ce ne ina tsammanin ka biya ni bashi da ka karba kuma idan ka ƙi biya kuma na zo karɓar kaddarar da ka jinginar kada ka ce min wai kana da kariya domin kai kasa ne mai ƴanci."

Ya ce wannan rubutun garanti ne kawai na cewa za mu biya bashin. "Na yi takaicin yadda wasu ke yi masa mummunan fasara."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel