Da duminsa: Gwamonin Najeriya 2 sun warke daga cutar Coronavirus rana daya

Da duminsa: Gwamonin Najeriya 2 sun warke daga cutar Coronavirus rana daya

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode John Fayemi tare da takawaransa na jihar Ebonyi, Dave Umahi sun samu waraka daga muguwar cuta mai toshe numfashi watau Coronavirus.

Gwamnonin sun bayyana hakan ne bayan gwajin karshe da aka yimusu ya nuna cewa sun barranta daga cutar.

Shi gwamnan Ebonyi ya sanar ne a jawabin da ya saki ranar Juma'a inda ya bayyana cewa shi, diyarsa, da wasu hadimansa uku da suka kamu da cutar sun warke.

Ya mika godiyarsa ga Allah, sannan al'ummar jiharsa bisa addu'o'insu da goyon baya.

Ya samu waraka bayan kimanin kwanaki 27 yana jinya. Za ku tuna cewa a ranar 7 ga Yuli ya sanar da harbuwarsa da cutar.

Da duminsa: Gwamonin Najeriya 2 sun warke daga cutar Coronavirus rana daya
Da duminsa: Gwamonin Najeriya 2 sun warke daga cutar Coronavirus rana daya
Asali: Twitter

A bangaren gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya sanar da samun warakarsa a shafinsa na Tuwita, da safiyar Asabar, 1 ga watan Agusta, 2020.

Yace: "Bayan kwanaki 11 a killace, na samu labari mai dadi cewa sakamako na ya fito na waraka. Ina mai godya ga Allah, iyalaina, ma'aikatan jinya na, da dukkan abokan arziki bisa addu'o'insu. "

"Wajibi ne mu cigaba da yin dukkan mai yiwuwa domin yakar annobar nan."

Da duminsa: Gwamonin Najeriya 2 sun warke daga cutar Coronavirus rana daya
Da duminsa: Gwamonin Najeriya 2 sun warke daga cutar Coronavirus rana daya
Asali: Facebook

A bangare guda, Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 462 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:37 na daren ranar Juma'a 31 ga Yulin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 462 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

FCT-93

Lagos-78

Plateau-64

Kaduna-54

Oyo-47

Ondo-32

Adamawa-23

Bauchi-19

Rivers-9

Ogun-9

Delta-9

Edo-7

Kano-6

Enugu-6

Nasarawa-5

Osun-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Juma'a 31 ga Yulin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 43,151 .

An sallami mutum 19,565 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 879.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel