Babbar Sallah: Ganduje ya saki fursunoni 29 a Kano

Babbar Sallah: Ganduje ya saki fursunoni 29 a Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya saki fursunoni 29 da ke zaman gidan gyaran hali na Dutsen-Goro a Kano.

Gwamnan da ya bayar da umurnin sakin fursunonin a yayin da ya kai ziyara gidan gyaran halin a ranar Juma'a ya ce ya aikata hakan ne saboda bikin babbar Sallah.

Ganduje ya ce an yi la'akari da irin laifukan da suka aikata da kuma alamun sauyin halayensu yayin zamansu a gidan gyaran halin.

Babbar Sallah: Ganduje ya yi wa fursunoni 29 afuwa
Babbar Sallah: Ganduje ya yi wa fursunoni 29 afuwa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa dalilin ziyarar shine don nuna wa fursunonin cewa gwamnati ta san da zamansu kuma suma mazauna jihar Kano ne.

DUBA WANNAN: Hotuna da bidiyo: Yadda Buhari da iyalansa suka yi Sallar Idi a Abuja

Amma, ya shawarci fursunonin da aka saki da kada su sake aikata wani laifi da zai sa su sake dawowa gidan.

Ya ce za a bawa kowannensu N5,000 da zai yi amfani da shi a matsayin kuɗin mota don ya koma garin su.

Shugaban gidan gyaran halin, Abdullahi Magaji ya yabawa Gwamna Ganduje saboda sakin fursunonin.

Magaji shima ya shawarci waɗanda aka saki su zama masu halaye na gari ta yadda ba za su sake dawowa gidan gyaran halin ba.

Mataimakin gwamnan, Nasiru Gawuna da wasu ƴan fadar gwamnati ne suka yi wa Ganduje rakiya zuwa gidan gyaran halin.

A wani rahaton, 'Yan sanda a jihar Katsina sun kashe wasu mutum uku da ake zargin 'yan bindiga ne yayin musayar wuta a cewar mai magana da yawun 'yan sandan jihar SP Gambo Isah kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

SP Isah ya ce, "Tawagar yan sandan ta bi sahun bata garin kuma ta rufe hanyar da za su bi su tsere ta ritsa su hakan ya saka aka yi musayar wuta tsakaninsu.

Tawagar yan sandan ta yi nasarar kashe yan bindiga uku, ta kwato bindiga kirar AK 47 da babura guda shida da 'yan bindigan suka tsere suka bari da shanu 17 da tumaki 40."

Ya kara da cewa, "A ranar 28/07/2020 misalin karfe 11 na dare, wasu yan bindiga masu yawa dauke da bindigu kirar AK 47 sun kai hari a kauyen Garin Zaki da ke karamar hukumar Batsari ta Jihar Katsina, sun fasa shaguna uku sun sace kaya masu yawa da a halin yanzu ba a kayyade kudinsu ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel