Yan Najeriya sun san na yi iyakan kokari na kan tsaro - Buhari

Yan Najeriya sun san na yi iyakan kokari na kan tsaro - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yan Najeriya sun san gwamnatinsa ta yi iyakan kokarinta wajen shawo kan matsalan tsaro da ake fama da shi a fadin tarayya.

Yayinda yake magana da manema labaran fadar shugaban kasa bayan Sallar Idi a fadar shugaban kasa Aso Villa, shugaban kasan yace ba lokacinsa aka fara fuskantar matsalar tsaro ba.

Amma ya nuna bacin ransa kan gazawan hukumomin tsaro , inda yace ya kamata a ce sun fi hakan kokari, The Cable ta ruwaito.

Yace: "Ina son yan Najeriya su farga kan kasarsu kuma su san abinda muka gada lokacin da muka dau mulki a 2015 Boko Haram ne a Arewa maso gabas sannan barandanci a Kudu maso kudu.... Yan Najeriya sun san munyi iyakan kokarinsu."

"Abinda ke faruwa a Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya na da matukar takaici amma nayi imanin cewa Sojoji, yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su kara kokari."

A jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya saki, ya ce Buhari ya tabbatarwa hukumomin tsaro cewa zai kara musu dukiya domin kawar da matsalar tsaron kasar nan.

Ya ruwaito Buhari cewa duk da cewan an samu nasarori da dama, akwai sauran aiki a gaba.

KU KARANTA: Hanyoyi hudu da za a iya amfani da su don adana naman sallah

Yan Najeriya sun san na yi iyakan kokari na kan tsaro - Buhari
Yan Najeriya sun san na yi iyakan kokari na kan tsaro - Buhari
Asali: Facebook

A bangare guda, Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiu Bagudu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya cika alkawuran da ya yiwa yan Najeriya lokacin da yake yakin neman zabe a 2015.

Gwamna ya bayyana hakan a jawbain Sallan da yayi ranar Juma'a a Birnin Kebbi, inda yace lamarin tsaro ya fi kyau yanzu fiye da lokacin da ya hau ragamar mulki.

Kan lamarin yaki da rashawa kuwa, ya ce Najeriya ta samu nasara wajen dakile masu cin hanci da rashawa.

Bagudu ya yabawa shugaba Muhammadu Buhari kan irin amincewar da yake da dan jihar Kebbi, wanda yake ministan shari'a kuma Antoni Janar, Abubakar Malami.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel