Tikitin Tinubu-Dogara a 2023 jita-jita ne kawai, babu gaskiya ciki - Shugaban jam'iyyar APC

Tikitin Tinubu-Dogara a 2023 jita-jita ne kawai, babu gaskiya ciki - Shugaban jam'iyyar APC

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya siffanta maganar tikitin neman shugabancin kasan jigon jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, da tsohon kakakin majalisa, Yakubu Dogara, a matsayin mataimakinsa a 2023 matsayin jita-jita kawai.

Mai Mala Buni, wanda shine shugaban kwamitin rikon kwaryan jan'iyyar All Progressives Congress, APC ya bayyana hakan ne yayin hirarsa da BBC Hausa ranar Alhamis a Kaduna.

Yace: "Ka san ba zaka iya hana mutane magana ba. Kana jita-jita na tasiri a demokradiyya. Wannan ba shi bane matsalanmu yanzu. Matsalanmu yanzu shine hada kan jam'iyyar."

Kan zaben jihar Edo, Buni ya ce jam'iyyar APC za ta bada mamaki. Ya ce jam'iyyar za ta samu nasara kuma zata lashe zaben da tazara mai yawa.

Zaben, da za'a gudanar ranar 19 ga Satumba, tsakanin yan takara 17 musamman Godwin Obaseki na PDP da Osaze Ize-Iyamu na APC.

Tikitin Tinubu-Dogara a 2023 jita-jita ne kawai, babu gaskiya ciki - Shugaban jam'iyyar APC
Tikitin Tinubu-Dogara a 2023 jita-jita ne kawai, babu gaskiya ciki - Shugaban jam'iyyar APC
Asali: UGC

Za ku tuna cewa Hanarabul Yakubu Dogara ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a makon da ya gabata inda ya gana da shugaba Buhari.

Kimanin kwanaki hudu bayan sauya shekarsa, Yakubu Dogara, a ranar Litnin ya jagoranci wasu mambobin majalisa zuwa gidan gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.

Tawagar sun gana da Buni, wanda shine shugaban kwamitin rikon kwaryan All Progressives Congress (APC), don tattaunawa kan yiwuwan sauya shekansu.

Yan majalisan da Yakubu Dogara ya jagoranta zuwa gidan Buni sune Danjuma Usman Shidda (APGA, jihar Taraba), Sam Izuigbo (Anambra); Hembe Hembe (Benue) da wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Bauchi, Alhaji Saidu.

Shugaban kwamitin yardaddun jam'iyyar PDP, Sanata Walid Jubrin, ya bayyana cewa Kokarin samun kujerar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ne yasa tsohon kakakin ya koma jam'iyyar APC.

Ya bayyana hakan a takarda da ya fitar a Abuja a ranar Litinin, jaridar The Nation ta ruwaito.

Yace: "Ina tsammanin tsohon kakakin majalisar yana da wata manufa daban da ta sa ya koma APC. Ina tsammanin kujerar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa yake hange a 2023 a karkashin jam'iyyar APC wanda ya san ba zai taba samu ba a PDP."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel