Zulum ya kai wa ƴan gudun hijira 80,000 tallafi a Monguno (Hotuna)
Duk da harin da aka kai wa tawagarsa a garin Baga, Gwamna Babagana Umara Zulum ya cigaba da ayyukan jin kansa a Munguno inda ya kai wa yan sansanin gudun hijira kimanin 80,000 kayan tallafi.
Gwamnan ya isa Munguno a ranar Litinin tare da tawagarsa inda suka raba wa 'yan sansanin gudun hijira kayan tallafi a Marte, Guzamala, Kukawa, Nganzai da Monguna.
An rabar da dubban buhunnan hatsi, man girki da wasu kayayyakin da mutanen da ke sansanin yan gudun hijirar da sauran mabukata a garuruwan da sansanin suke.

Asali: Facebook
An raba wa mazaje buhunnan hatsi da man gyada yayin da mata kuma kowannensu aka bata N5,000.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba
Kwamandan rundunar Soji da ke barikin sojoji ta Nasara a Monguna ya yabawa jajircewa irin ta Gwamna Zulum bisa ziyarar da ya kai wa sojojin.

Asali: Facebook
Kafin ya bari Monguna zuwa Maiduguri, Farfesa Zulum ya duba wasu ayyuka da ake gudanarwa da suka hada da ginin Babban Makarantar Sakandare ta Islamiyya, ginin gidaje 1000 da ginin babban makarantar frimare.

Asali: Facebook
Da ya ke wurin aikin ginin gidajen 1000 da Babban Makarantar Sakandare ta Islamiyya, Zulum ya bukaci 'yan kwangilar su cigaba da aiki mai kyau da suka fara.
"Na ga aikin ku a Uyo, na gani a Mbala. Ban gamsu da irin aikin da na ke gani a nan ba. Ya kumata mu janyo hankalinka game da ingancin aikin. Ba wai ginin kadai bane damuwarsu, muna son aiki mai kyau."
A wani rahoton, kun ji rundunar Soji za ta fara bincike a kan harin da aka kai wa tawagar Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Laraba a cewa Kakakin Soji, Sagir Musa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.
Musa ya ce wasu da ake zargin yan ta'adda ne suka kai wa tawagar gwamnan hari a hanyarsu ta zuwa garin Baga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce Zulum ya ziyarci Kwamandan Brigade ta 19 na Rundunar Soji da ke Sansanin Baga inda ya yi masa bayani a kan halin tsaro na yankin baki daya.
A cewarsa, mummunan lamarin ya faru ne jim kadan bayan gwamnan da tawagarsa sun bar sansanin ta sojojin da ke Baga za su ziyarci wasu yankuna a garin ta Baga.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng