Rundunar Soji ta fara bincike kan harin da aka kai wa tawagar Zulum

Rundunar Soji ta fara bincike kan harin da aka kai wa tawagar Zulum

- Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta fara gudanar da bincike game da harin da aka kaiwa tawagar Gwamna Zulum

- A ranar Laraba ne wasu da ake zargin yan taadda ne suka kai wa tawagar Gwamna Zulum hari a garin Baga yayin ziyara da ya kai

- Kakakin Rundunar Soji, Sagir Musa ya ce ana can ana bincike a yankin da niyyar gano maharan domin a hukunta su

Rundunar Sojin Najeriya za ta fara bincike a kan harin da aka kai wa tawagar Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Laraba a cewa Kakakin Soji, Sagir Musa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.

Musa ya ce wasu da ake zargin yan ta'adda ne suka kai wa tawagar gwamnan hari a hanyarsu ta zuwa garin Baga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rundunar Soji ta fara bincike kan harin da aka kai wa tawagar Zulum
Babagana Zulum. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba

Ya ce Zulum ya ziyarci Kwamandan Brigade ta 19 na Rundunar Soji da ke Sansanin Baga inda ya yi masa bayani a kan halin tsaro na yankin baki daya.

A cewarsa, mummunan lamarin ya faru ne jim kadan bayan gwamnan da tawagarsa sun bar sansanin ta sojojin da ke Baga za su ziyarci wasu yankuna a garin ta Baga.

"Lamarin ya tilastawa gwamnan soke ziyarar da ya yi niyyar kaiwa a wasu sassan na Baga.

"Duk da cewa a halin yanzu babbu cikaken bayani a kan hari duba da cewa ana bincike, ana nan ana kokarin bincike yankin da abin ya faru da niyyar gano wadanda suka kai harin."

"An kuma fara gudanar da bincike domin gano abinda ya yi sanadin afkuwar harin," a cewar Kakakin rundunar sojin.

Musa, ya ce harin abin takaici ne duk da cewa a halin yanzu hankulan mutanen garin ya kwanta kuma sun cigaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel