Katsina: 'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 3, sun kama wasu biyu

Katsina: 'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 3, sun kama wasu biyu

- An yi arangama tsakanin 'yan bindiga da tawagar yan sanda a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina

- Jamian yan sandan sunyi nasarar kashe 'yan bindiga uku, sun kama biyu sun kuma kwato kayayyaki

- Kayayyakin da jami'an 'yan sandan suka kwato sun hada da bindigu, shanu 17 da tumaki 40

'Yan sanda a jihar Katsina sun kashe wasu mutum uku da ake zargin 'yan bindiga ne yayin musayar wuta a cewar mai magana da yawun 'yan sandan jihar SP Gambo Isah kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

SP Isah ya ce, "Tawagar yan sandan ta bi sahun bata garin kuma ta rufe hanyar da za su bi su tsere ta ritsa su hakan ya saka aka yi musayar wuta tsakaninsu.

Katsina: 'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 3, sun kama wasu biyu
Yan sanda. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba

"Tawagar yan sandan ta yi nasarar kashe yan bindiga uku, ta kwato bindiga kirar AK 47 da babura guda shida da 'yan bindigan suka tsere suka bari da shanu 17 da tumaki 40."

Ya kara da cewa, "A ranar 28/07/2020 misalin karfe 11 na dare, wasu yan bindiga masu yawa dauke da bindigu kirar AK 47 sun kai hari a kauyen Garin Zaki da ke karamar hukumar Batsari ta Jihar Katsina, sun fasa shaguna uku sun sace kaya masu yawa da a halin yanzu ba a kayyade kudinsu ba."

A yayin bincike, ya ce an bi sahun takalman yan bindigan zuwa gidan wani mutum mai shekaru 50, Abubakar Ibrahim Maude a kauyen Babban Duhu da ke karamar hukumar Safana.

An gudanar da bincika gidansa an kuma gano wasu daga cikin kayayakin da aka sace a shagunan kuma a halin yanzu ana cigaba da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel