Babbar Sallah: Shugaba Buhari ya yi sabon gargadi a kan COVID-19

Babbar Sallah: Shugaba Buhari ya yi sabon gargadi a kan COVID-19

Shugaba Buhari a ranar Alhamis ya ce annobar coronavirus ta saka mutane ba za su iya taruwa a masallatai suyi ibada kamar yadda suka saba ba, hakan yasa ya shawarci su bi dokokin kwararu don kiyaye lafiyarsu.

A sakonsa na Sallah, Buhari ya yi kira ga alummar musulmi su cigaba da yin hakuri da fahimta bisa matsin da dokokin kiyaye yaduwar annobar ka iya janyo wa a rayuwarsu musamman a bangaren ibada.

Babbar Sallah: Shugaba Buhari ya yi sabon gargadi a kan COVID-19
Babbar Sallah: Shugaba Buhari ya yi sabon gargadi a kan COVID-19
Asali: Twitter

"Coronavirus ya janyo tsaika ga zamantakewar mu, tattalin arziki da ibada. Dokokin da muka saka na dakile yaduwar cutar ya takaita yadda mutane ke taruwa a masallatai da coci coci.

DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba

"Duk wata doka da aka saka na dakile wannan cutar ta haifar wani abu a rayuwar mu. Saboda haka ina kira da musulmi da sauran mabiya addinai su cigaba da hakuri a yayin da muke daukan matakan kare lafiyar alummar mu.

"Babu wata zababiyar gwamnati da za ta hana mutane ikon yin ibadunsu da gangan ta hanyar takaita adadin mutanen da za su hallarci wurin ibadun.

"Saka wadannan dokokin ya zama dole ne saboda kiyaye lafiyar alumma saboda haka a dena ganinsa kamar wani mataki ne na dakile wa mutane damarsu ta yin ibada."

Shugaban da a baya ya sanar da cewa ba zai karbi gaisuwar sallah ba daga mutane a fadarsa don biyaya ga dokokin kiyaye yaduwar annobar ya yabawa musulmi da kirista saboda biyyaa ga dokokin kiyaye korona.

Ya bayar da tabbacin cewa, "A bangaren mu za mu cigaba da bayar da tallafi ga mutane domin takaita wahalhalun da suka shiga sakamakon dokokin da muka saka.

Buhari ya tunatar da alumma cewa korona ta shafi kasashen duniya kuma an rufe masallatai da coci coci a kasashen domin kiyaye lafiyar mutane.

A yayin da ya ke taya musulmin murna, shugaban kasar ya yi kira gare su da kada su manta darrusan da suke tattare da sallar ta Eid-el Kabir.

"Musulmi su yi koyi da kyawawan halayen annabawan mu domin kara kusantar ubangiji da gudanar da ibadojinsu.

"Za mu samu nasara a rayuwar mu idan muna aikata koyarwan addinin mu. Duk abinda muke yi a rayuwa, ya kamata mu saka tsoron Allah domin samun cigaba a rayuwar mu da alumma baki daya."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel