Jerin jihohin Arewan da aka hana bukukuwan Sallah

Jerin jihohin Arewan da aka hana bukukuwan Sallah

Yayinda mabiya addinin Islama ke murnar bikin Eidul Kabir yau Juma'a, 31 ga watan yuli, gwamnatocin wasu jihohi sun hana bukukuwan Sallah domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a kasa.

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnoni su kafa dokar hana bukukuwan murnar Sallan domin hana mayar da hannun agogo bayan wajen yaki da annobar.

Tuni wasu gwamnonin Arewa suka amda kiran gwamnatin tarayya kuma suka dakatad da bukukuwan Sallah, har da hana Sallari Idi a wasu.

Ga jerin jihohin da aka hana bukukuwan Sallah bana:

1. Jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano a ranar Laraba ta sanar da dakatad da duk wani bikin murnar Sallah da aka saba jihar.

Gwamnatin ta ce an yanke shawaran haka ne domin habaka nasarorin da aka samu wajjen yakar da cutar Coronavirus.

2. Jihar Plateau

An hana Sallan Idi a jihar Plateau: A ranar Laraba hukumar yan sandan jihar ta ce babu Sallar Idi a jihar Plateau bana.

A jawabin da kakakin hukumar, ASP Ubah Gabriel, ya saki, ya ce an yanke shawaran haka ne biyo bayan ganawar hukumomin tsaro, shugabannin addini, da wasu masu ruwa da tsaki a jihar.

Amma hukumar tace za'a iya Sallar Idin a unguwanni da sharadin kada adadin mamu ya wuce 50.

3. Birnin tarayya Abuja

Ministan birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, ya ce jama'a su gudanar da Sallolin idinsu a cikin Masallatai domin takaita yaduwar cutar COVID19.

A takardar da sakataren yada labaran, Tony Ogunleye, ya saki, minista ya bada umurnin haka ne bayan ganawa tsakanin FCTA da shugabannin Limaman Abuja, karkashin jagoranincn Imam Tajudden Bello.

4. Jihar Osun

Gwamnatin jihar Osun ta dakatad da Sallar Idi a jihar, Sakataren gwamnatin jihar, Wole Oyebamijin yace an dau matakin ne don takaita yaduwar cutar Korona.

5. Jihar Neja

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya dakatad dukkan bukukuwan Sallan da aka saba a dukkan masarautun jihar takwas. A jawabin da sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Matane, ya saki, ya ce an amince a gudanar Sallar Idi amma bisa sharrudan da aka gindaya.

6. Jihar Kwara

Gwamnatin jihar Kwara, ta dakatad da Sallolin Idi a jihar. Mataimakin gwamnan jihar, Kayode Alabi, ya bayyana hakan ne ga manema labarai.

Ya ce an hana Sallah ne saboda akwai yiwuwan taruwa mutane zai iya sabbaba yaduwar cutar Korona.

7. Jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta dakatad da dukkan bukukuwan Sallah a jihar. Amma gwamnatin ta amince a gudanar da Sallolin Idi kamar yadda aka saba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel