Sallah: Buhari ya mika sako mai muhimmanci ga daukacin Musulmin Najeriya

Sallah: Buhari ya mika sako mai muhimmanci ga daukacin Musulmin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jaddada kiransa ga 'yan Najeriya da su ci gaba da hakuri tare da nuna fahimtarsu a kan dokokin da ake saka musu don dakile yaduwar annobar korona, ballantana a wuararen bauta.

A sakon barka da Sallah da ya mika ga daukacin Musulmin Najeriya, Shugaba Buhari ya ce barkewar annobar korona ta sa jama'a basu iya taruwa a wuraren bauta kamar yadda suke yi.

Ya yi kira ga masu bauta da su kiyaye dokokin dakile yaduwar annobar garesu da masoyansu.

"Cutar korona ta saka jama'a cikin mawuyacin hali ta yadda ta hana tattalin arziki, walwala da bauta.

"Dokokin dakile cutar da muka samar sun hana jama'a walwala wacce ba za ta bari a hadu a yi bauta ba a masallatai da majami'u.

“Kowanne mataki da aka saka don dakile cutar ba a saka su ba don takura jama'a. A don haka muke kira ga Musulmi da sauran jama'a da su ci gaba da nuna fahimta ga gwamnati don kiyaye kai.

“Babu wata zababbiyar gwamnati da za ta dakile walwalar jama'arta ta hanyar hana jama'a zuwa wuraren bauta.

Sallah: Buhari ya mika sako mai muhimmanci ga daukacin Musulmin Najeriya
Sallah: Buhari ya mika sako mai muhimmanci ga daukacin Musulmin Najeriya. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda dan sanda ya dinga lalata da ni tun dare har asuba - Matar da ta take doka

"An saka wadannan dokokin ne don tsare lafiyar jama'a, don haka kada a kalle a a matsayin takurawa," yace

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa Musulmi da Kiristoci da ke kiyaye dokokin COVID-19 don jama'a.

Ya tabbatar da cewa, "A bangarenmu, za mu ci gaba da samar da tallafi don rage wa jama'a radadin halin da suke ciki a yayin da suke kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar."

Shugaban kasar ya tunatar da masu bauta cewa annobar korona ruwan dare ce dame duniya, wacce tsa aka rufe masallatai da majami'u, yayin da aka kafa dokar nesa-nesa da juna.

A yayin da yake wa Musulmi fatan yin sallah cikin walwala, shugaban kasar ya yi kira ga masu bauta da kada su manta da amfanin babbar sallar.

Ya kara da cewa, "Musulmai su yi koyi da kyawawan halayyyar Annabi don kara kusanci ga Ubangiji. A duk abinda muke yi a rayuwa, dole ne mu saka tsoron Allah."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng