Boko haram: Zulum ya bayyana mataki mai tsauri da zai dauka

Boko haram: Zulum ya bayyana mataki mai tsauri da zai dauka

Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya ce idan rundunar sojin Najeriya ba za su iya tsare Baga ba, zai sa mafarauta su tsare masa garin.

A ranar Laraba, mayakan ta'addancin Boko Haram sun kai wa tawagar gwamnan farmaki a yayin da take kan hanyar ziyartar sansanin 'yan gudun hijira da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar.

Bayan bada motocin sintiri 12 ga jami'an tsaro a yankin, Zulum ya kaddamar da sake bude babbar hanyar Monguno zuwa Baga bayan rufeta da aka yi na shekaru biyu.

Zulum, wanda tun farko ya yi jawabi ga rundunar sojin a kan cewa babu 'yan ta'addan a Baga, ya koma inda ya tambayesu yadda aka hari tawagarsa.

"Rundunar suna kusa a mil 4 fiye da shekara daya, akwai zagon kasa a al'amarin. Matsalar ba daga shugaban kasa Muhammadu Buhari bane ko Janar Buratai. Matsalar daga tsarin ne. Akwai bukatar a sake duba shi.

"Muna da sama da 'yan gudun hijira 80,000 a Monguno, ba za su ci gaba da dogara da kungiyoyin taimakon kai da kai wurin samun abinci.

"Dole ne mu samar musu da yadda za a yi su koma gidajensu kuma su ci gaba da kasuwanci da noma.

Boko haram: Zulum ya bayyana mataki mai tsauri da zai dauka
Boko haram: Zulum ya bayyana mataki mai tsauri da zai dauka. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Facebook

KU KARANTA: Harin tawagar Zulum: Gwamnan Borno ya huce fushinsa a kan dakarun soji (Bidiyo)

“Bayan sallah, za mu koma Kukawa. Za mu bai wa rundunar sojin lokaci amma idan basu kwato Baga ba, za mu saka mafarauta da 'yan sa kai su kwato mana Baga. Ba za mu ci gaba da zama haka ba. Makomar jama'armu a hannunmu take," yace.

A yayin martani game da harin, Sagir Musa, kakakin rundunar sojin ya ce har yanzu babu bayani gamsasshe a kan a lamarin kuma ana kokarin duba yankin.

"Ana bincike a kan aukuwar lamarin da ya kawo harin," yace.

Ya kara da cewa, “Abun takaicin, wurin kebabbe ne inda abun ya faru kuma tun bayan dawowar zaman lafiya,, hakan bata sake faruwa ba.

"Rundunar sojin Najeriya na son tabbatar wa da jama'a cewa za a shawo kan lamarin ta yadda hakan ba zai sake aukuwa ba nan gaba."

Sama da watanni da suka shude, gwamnan ya saba arangama da dakarun sojin da ke jihar. A watan Janairu, ya zargi rundunar da karbar kudi daga masu amfani da tituna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel