'Iyayena sun sallamani, sun ce kar na sake na koma gidansu' - Matashiyar da ta shiga fim

'Iyayena sun sallamani, sun ce kar na sake na koma gidansu' - Matashiyar da ta shiga fim

Dorathy Bachor, matashiyar nan da ke cikin shirin gidan talabijin mai taken BBNaija, ta ce iyayenta sun sanar da ita cewa kar ta sake ta koma gidansu idan an kammala wasan kwaikwayon.

Matashiyar, wacce ta kasance daya daga cikin 'yan wasa 20 da ke cikin shirin BBNaija na shekarar 2020, ta bayyana hakan ne ranar Talata yayin hira da ita a kan shirin wasan 'Big Brother' wanda ta ke ciki.

Ta bayyana hakan ne yayin da ta ke amsa tambaya a kan ko tana ganin cewa za ta iya lashe kyautar miliyan N85 da za a bawa duk wanda ya zama gwarzo a karshen shirin.

Dorathy, 'yar duma - dumar budurwa, ta ce ta na fatan za ta lashe kyautar makudan kudaden, saboda hakan ne kadai zai sa iyayenta su sauya matakin da suka dauka na cewa sun sallamata, kar ta koma mu su gida bayan shirin.

A cikin shirin BBNaija, ana tattara 'yan gayun matasa maza da mata tare da killacesu a wani gida na alfarma domin su yi rayuwa tare kamar da gaske a yayin da ake nadar bidiyon duk abubuwan da su ke yi.

'Iyayena sun sallamani, sun ce kar na sake na koma gidansu' - Matashiyar da ta shiga fim
Matashiya Dorathy Bachor
Source: Instagram

Jama'a da dama na yawan sukar shirin tare da bayyana rashin jin dadinsu a kan yadda shirin ke jan hankali matasa musamman mata tare da gurbata tarbiyarsu.

DUBA WANNAN: Tubabben dan Boko Haram da gwamnati ta saki ya kashe mahaifinsa ya kwashi dukiya ya gudu

Ma su sukar shirin na kafa hujja da cewa ana nuna zallar rashin kunya da batsa kiri-kiri a cikin shirin.

Samun damar shiga shirin wasan fim din BBNaija ya kasance burin matasa da yawa, musammam a yankin kudancin Najeriya.

Ma su kwadayin shiga shirin fim din su na hangen irin makudan miliyoyin da za a bawa wanda ya zama gwarzo a karshen shirin.

An fara nuna shirin BBNaija a gidan talabijin a shekarar 2006.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel