'Yan bindiga sun kai wa motar kudi hari, sun kashe 'yan sanda 4

'Yan bindiga sun kai wa motar kudi hari, sun kashe 'yan sanda 4

Wasu 'yan bindiga a ranar Laraba sun kai wa motar kudi hari a jihar Ebonyi inda suka kashe 'yan sanda hudu da ke raka motar.

An gano cewa 'yan bindigar sun yi yunkurin kwashe kudin motar ne yayin da suka tsareta a Ezzamgbo a karamar hukumar Ohaukwu.

Motar ta dauko kudi ne daga Enugu zuwa Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

'Yan fashin sun yi yunkurin tsare motar ne tare da yin awon gaba da kudin da ke ciki. Sun fara harbin motar jami'an tsaron da ke tafe tare da motar kudin.

'Yan sanda hudu suka rasa rayukansu yayin da biyu suka samu miyagun raunika.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Philip Maku, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kamar yadda yace, 'yan fashin sun bibiyi motar kudin tun daga jihar Enugu.

Ya ce 'yan fashin basu yi nasarar kwashe kudin motar ba saboda direban ya yi jarumtar tserewa da ita.

"Sun lalata daya daga cikin tayoyin motar kudin amma direban sai da yayi nasarar tserewa da ita. Sun kasa bin direban saboda ya nufa wurin sojojin da ke kan hanya," yace.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce 'yan sanda biyu da suka samu raunikan na samun kulawa yayin da gawawwakin hudun ke ma'adanar gawawwaki.

Maku ya ce 'yan sanda sun fara kokarin damko 'yan fashin da suka tsere.

'Yan bindiga sun kai wa motar kudi hari, sun kashe 'yan sanda 4
'Yan bindiga sun kai wa motar kudi hari, sun kashe 'yan sanda 4. Hoto daga Premium Times
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Mpeni Kofi: Bishiya mai shekaru 300 da ake zargin tana komawa mutum tsakar dare

A wani labari na daban, wani mutum dan asalin kasar Nijar wanda ake zargin yana samar wa da 'yan bindiga makamai ya sha mugun duka a hannun jama'a. An samu gawarsa a cikin wani rafi da ke karamar hukumar Gada ta jihar Sokoto.

Kamar yadda wata takarda da ta fito daga kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ya fitar, ya ce a ranar 26 ga watan Yuli, bayanai sun isa hedkwatar 'yan sandan jihar a kan gawa da aka gani ta wani dan asalin Nijar.

Ana zarginsa da samar da makamai ga 'yan bindiga, kuma an tsaresa ne a kauyen Diboni da ke karamar hukumar Gada a kan hanyarsu ta zuwa Zamfara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel