Nigeria da Amurka sun cimma matsaya kan yarjejeniyar sufurin jiragen sama

Nigeria da Amurka sun cimma matsaya kan yarjejeniyar sufurin jiragen sama

- Gwamnatin Nigeria ta amince da sa hannu kan wata jarjejeniya ta sufurin jiragen sama, tsakanin Nigeria da gwamnatin kasar Amurka

- Ministan watsa labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce yarjejeniyar zata bunkasa tattalin arziki, ci gaban rayuwa da al'adu na kasashen

- An kawo bukatar sa hannu kan wannan yarjejeniya tun a wani taro da aka gudanar a Chicago a ranar 7 ga watan Disamba, 1994

Gwamnatin Nigeria ta amince da sa hannu kan wata jarjejeniya ta sufurin jiragen sama, tsakanin Nigeria da gwamnatin kasar Amurka.

Ministan watsa labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban kasa.

Ya yi jawabin ne bayan fitowa daga taron majalisar zartaswa karo na 10 da aka gudanar ta yanar gizo wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Mohammed, wanda ya yi magana a madadin ministan sufuri, Sanata Hadi Sirika, ya ce yarjejeniyar zata bunkasa tattalin arziki, ci gaban rayuwa da al'adu na kasashen biyu.

A cewarsa: "Ministan sufuri ya gabatar da wata takarda a yau (Laraba) inda ya bukaci a sa hannu kan yarjejeniyar sufurin jiragen sama tsakanin Nigeria da Amurka.

"Ministan ya bukaci amincewar majalisar domin sa hannu kan wannan yarjejeniya wacce take da muhimmanci wajen bunkasa alakar Nigeria da USA.

"Za ku iya tunawa cewa da Amurka da Nigeria abokan juna ne a taron Chicago da aka yi a ranar 7 ga watan Disamba, 1994.

"Tambihi na 6 na taron ya kawo bukatar kasashe su sa hannu kan yarjejeniyar sufurin jiragen sama domin bunkasa alaka ta siyasa, tattalin arziki da bunkasa rayuwa.

KARANTA WANNAN: Dan wasan Nigeria, Victor Osimhen ya kulla yarjejeniya da Napoli a kan €80m

Nigeria da Amurka sun cimma matsaya kan yarjejeniyar sufurin jiragen sama
Nigeria da Amurka sun cimma matsaya kan yarjejeniyar sufurin jiragen sama
Asali: Twitter

"Tuni kasar Amurka ta sa hannu a nata bangaren, kuma a yau shugaban kasa da kafatanin majalisar sun amince kuma sun sa hannu kan yarjejeniyar.

"Don haka, shugaban kasa ya rattaba hannu kan yarjejeniyar sufurin jiragen sama tsakanin Nigeria da Amurka da nufin amfanar kasashen biyu, musamman ma Nigeria a kokarinta na ganin ta mallakin nata kamfanin jirgin sama.

"Don haka, zamu yi amfani da wannan damar wajen bunkasa tattalin arziki, al'adu da bunkasa rayuwa tsakaninmu da Amurka."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel