Jama'ar Sokoto sun kashe wani dan Nijar da ake zargin yana kawowa 'yan bindiga makamai

Jama'ar Sokoto sun kashe wani dan Nijar da ake zargin yana kawowa 'yan bindiga makamai

Wani mutum dan asalin kasar Nijar wanda ake zargin yana samar wa da 'yan bindiga makamai ya sha mugun duka a hannun jama'a. An samu gawarsa a cikin wani rafi da ke karamar hukumar Gada ta jihar Sokoto.

Kamar yadda wata takarda da ta fito daga kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ya fitar, ya ce a ranar 26 ga watan Yuli, bayanai sun isa hedkwatar 'yan sandan jihar a kan gawa da aka gani ta wani dan asalin Nijar.

Ana zarginsa da samar da makamai ga 'yan bindiga, kuma an tsaresa ne a kauyen Diboni da ke karamar hukumar Gada a kan hanyarsu ta zuwa Zamfara.

"Ambaliyar ruwa ce ta tsaresa sakamakon mamakon ruwan saman da aka yi. Wanda ake zargin ya bukaci jama'ar yankin da su taimaka masa don tsallake ruwa inda wani buhun da ke kan babur dinsa ya zama abun zargi.

"Mazauna kauyen sun tirsasa shi inda suka nemi bude buhun amma wanda ake zargin ya ki amincewa da hakan.

"Ta karfin tsiya suka bude inda suka ci karo da makamai wanda hakan yasa mazauna kauyen suka masa duka tare da kona shi sannan suka saka shi a rafi," yace.

Jama'ar Sokoto sun kashe wani dan Nijar da ake zargin yana kawowa 'yan bindiga makamai
Jama'ar Sokoto sun kashe wani dan Nijar da ake zargin yana kawowa 'yan bindiga makamai. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mpeni Kofi: Bishiya mai shekaru 300 da ake zargin tana komawa mutum tsakar dare

Sadiq ya ce bayan samun bayanan, DPO na Gada ya jagoranci tawagar jami'an tsaro zuwa inda abun ya faru. Sun samu harsasai 3,144 na bindiga AK 47 da kuma babur kirar Kasea mara rijista.

Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar Sokoto, CP Ibrahim S. Kaoje ya umarci sashen binciken manyan laifuka da su fara bincike a kan lamarin sannan su tabbatar da an gano ko waye mutumin.

A wani labari makamancin hakan, hedkwatar tsaro ta kasa ta ce rundunar soji ta Operation Sahel Sanity ta yi nasarar halakawa tare da kama 'yan bindiga masu tarin yawa, masu satar shanu, masu garkuwa da mutane da sauran 'yan ta'adda a yankin arewa maso yamma.

Mukaddasin daraktan yada labarai na hedkwatar tsaron, Birgediya janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan ne a wata takardar da ya fitar a ranar Litinin a garin Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel