Yanzu-yanzu: Jami'an yan sanda sun damke barayi da masu garkuwa da mutane 35 (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Jami'an yan sanda sun damke barayi da masu garkuwa da mutane 35 (Hotuna)

Jami'an yan sanda rundunar IRT sun damke wasu yan baranda 35 a fadin tarayya kan laifin aikata fashi da makami da garkuwa da mutane.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter da yammacin Laraba, 29 ga Yuli, 2020.

Daga cikin wadanda aka damke akwai wasu yan ta'addan Fasto, Adetokumbo Adenopo, shugaban cocin New Life Ministry, Lukosi, dake Shagamu, jihar Ogun tare da abokan aikinsa uku,Chigozie Williams, Ugoji Linus, da Emmanuel Chris Ani.

Sun aikata laifin garkuwa da wani Jonathan Ekpo daga jihar Benue.

Hakazalika, an damke wani Udodiri Bright da abokan aikinshi Ekwuru Shadrack aka Escobar, Chimerie Igwe aka 4real da Chibuike Sunday.

An damkesu ne ranar 5 ga Yuli 2020 da laifin garkuwa da kisan wani Sojan kasar AMurka, Chuks Okebata, wanda ya dawo Najeriya hutu a shekarar 2017.

A damkesu ne watanni 31 ana nemansa ruwa a jallo.

Yanzu-yanzu: Jami'an yan sanda sun damke barayi da masu garkuwa da mutane 35 (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Jami'an yan sanda sun damke barayi da masu garkuwa da mutane 35 (Hotuna)
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An sanar da ranar fara jarabawar NECO da NABTEB

Bugu da kari, Yan sandan sun damke wasu barayin motoci da suka shahara wajen kwacen motocin mutane karkashin jagorancin wani Yakubu Hayatu.

Sauran abokan fashinsa da aka damke sune Adamu Awalu, Abdulrahman Yakubu, Yusuf Adamu, Kamal Japhet, Abubakar Samaila, Muhammadu Abdulahi, Yahaya Mohammed, da Ibrahim Abubakar.

Bincike ya nuna cewa sun kwace sama da motoci 30 kuma sun kashe yan sanda biyu. Sun yi amfani da na'urar datse bibiyan motoci domin gujewa yan sanda kuma su sayarwa wani Alhaji Garba Maradi daga kasar Nijar.

Tuni an samu nasaran kwace motoci 18 da suka sace.

Daga cikin makaman da suka kwato akwai: bindiga AK47 4, FMC 1, PAG 1, karamin bindiga 1, carbin harsasai 4, dss.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel