An azabtar da matashi har ya mutu yayin gwajin shiga kungiyar asiri

An azabtar da matashi har ya mutu yayin gwajin shiga kungiyar asiri

Kotun gargajiya da ke zamanta a jihar Ebonyi ta umurci a bawa wani Nwali Kingsley, masauki a gidan gyaran hali a ranar Talata saboda kashe wani Nwafor Johnson yayin masa gwajin shiga kungiyar asiri.

An gano cewa wanda ake zargin da wasu da ake nema har yanzu sun kuma azabtar da wani Chigbo Ugbala da sanduna da adduna yayin gwajin ta shiga kungiyar asirin.

Punch Metro ta ruwaito cewa bayan Johnson ya mutu an jefa gawarsa a cikin rafi, Ugbala ya tsere daga wurin da ake gwajin shiga kungiyar asirin.

An azabtar da matashi har ya mutu yayin gwajin shiga kungiyar asiri
An azabtar da matashi har ya mutu yayin gwajin shiga kungiyar asiri
Asali: UGC

Wata majiya ta ce anyi kokarin gano gawar mamacin daga rafin amma ba ayi nasara ba.

DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba

Wakilin majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 10 ga watan Yuli a makatantar sakandare ta Ekeugwu-Azuinyaba da ke karamar hukumar Ishielu na jihar Ebonyi.

An gurfanar da Kingsley a kotun ana tuhumarsa da kisan kai, hadin baki, shiga kungiyar asiri da mallakar bindigu ba tare da izinin hukuma ba.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Eze Nnabuaku, ya shaidawa kotu cewa laifukan da ake tuhumarsa sun ci karo da sashi na 516A (a), 319 (1) da 335 ta Criminal Code Cap. 33 Vol. 1, ta jihar Ebonyi.

Wanda ake zargin da bai samu lauya mai kare shi a kotun ba ya ce abokansa ne suka jefa shi cikin harkar kuma ya nemi kotu ta yi masa sasauci.

Shugaban kotun, Mrs Nenna Onuoha ta ce kotun ba ta da ikon sauraron irin wannan karar.

Ta bukaci a turo bayannan shariar zuwa ofishin sauraron korafin al'umma sannan ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 7 ga watan Augustan 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel