Zimbabwe: Janar Perrance Shiri ya mutu bayan gajerar jinya a asibiti ya na shekara 65

Zimbabwe: Janar Perrance Shiri ya mutu bayan gajerar jinya a asibiti ya na shekara 65

Ministan harkar gona na kasar Zimbabwe, Janar Perrance Shiri, wanda ya taimaka wajen hambarar da gwamnatin Marigayi Robert Mugabe a 2017 ya rasu.

Mai girma shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya bada sanarwar mutuwar Perrance Shiri a ranar Laraba, 28 ga watan Yuli, 2020.

Perrance Shiri ya jagoranci sojojin saman kasar Afrikan na tsawon shekara da shekaru, kafin ya ajiye kayan soji ya shiga gwamnati a 2017.

Mnangagwa ya fitar da jawabin ta’aziyya, ya ce: “Shiri ainihin ‘dan kishin kasa ne, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen neman ‘yanci da bautar kasarsa.”

Rahotannin da ake samu daga jaridun kasar Zimbabwe su na cewa mutuwar tsohon ministan ba ta rasa nasaba da cutar mashako ta COVID-19 wanda har yanzu ta ke ta’adi.

KU KARANTA: Buhari: Babu yawon sallah zuwa fadar Shugaban kasa

Zimbabwe: Janar Perrance Shiri ya mutu bayan gajerar jinya a asibiti ya na shekara 65
Perrance Shiri Hoto: East African report
Source: Twitter

Kawo yanzu mutane 40 Coronavirus ta kashe a Zimbabwe daga cikin mutum akalla 2, 800 da su ka kamu da mugun ciwon.

Marigayi Shiri shi ne ya jagoranci dakarun sojojin da su ka hallaka masu fararen a yankin yammacin kasar Zimbabwe shekaru kusan 40 da su ka wuce.

Jam’iyyar adawa ta MDC ta zargi Janar Shiri da hannu wajen tada rikicin siyasa a 2008, a wancan lokaci Mugabe ya kasa fadi zagayen farko na zaben shugaban kasa.

Bayan haka, gidan yada labaran waje su na bayyana Marigayin wanda ya mutu a shekara 65 a matsayin mai hannu wajen sauke Mugabe daga kan mulki.

Mugabe ya rike kujerar Firayim Minista na shekaru bakwai daga 1980 zuwa 1987, daga baya ya zama shugaban kasar Zimbabwe, ya mutu ne a Satumban 2019.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel