'Yan bindiga sun kashe ƴan gida ɗaya su 13 a Kogi

'Yan bindiga sun kashe ƴan gida ɗaya su 13 a Kogi

'Yan bindiga sun kashe mutum 13 'yan gida daya a ranar Laraba a wani hari da suka kai da safe a garin Agudu da ke Bassa a karamar hukumar Kogi/koton-karfe na jihar Kogi.

Kwamishinan yan sanda na jihar Kogi, Ede Ayuba ya tabbatar wa manema labarai afkuwar wannan lamarin a ranar Laraba kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya kara da cewa sun kuma sake kashe mutum daya yayin da suka raunata mutum shida da a yanzu suke asibiti suna karbar magani.

'Yan bindiga sun kashe 'yan gida daya su 13 a Kogi
'Yan bindiga sun kashe 'yan gida daya su 13 a Kogi. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Kwamishinan ya ce sun amsa kira nan take bayan an sanar da su amma a lokacin da suka isa wurin yan bindigan sun tsere.

Ya ce a halin yanzu dai an samu zaman lafiya a garin kuma kowa ya cigaba da harkokinsa kamar yadda ya saba.

DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba

Ayuba ya ce akwai yiwuwar rikici tsakanin garuruwa da aka dade ana fama da shi a jiha ne ya janyo harin.

Ya bayyana harin a matsayin abin takaici, "domin an kashe Mai gida da iyalansa guda 12, mutum daya kadai ya tsira a gidan."

Ya kuma ce an kama wadanda suka kashe Innocent Ofodile, mutumin da ya ke da fitattacen Kantin Chucks Supermarket a Lokoja da aka kashe a hanyar Lokoja zuwa Abuja.

Ya ce an kama wani Victor Omogor daga nan kuma ya tona asirin sauran abokansa da ya ce sun aikata mummunan lamarin tare.

A cewar Omogor, daya daga cikin maaikatan mutumin da ke aiki a shagonsa ne ya umurci su kashe marigayin saboda ya ki taimaka masa da kudi a lokacin da mahaifinsa ya rasu.

A wani rahoton daban, Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Kano, Mr Habu A. Sani a ranar Talata ya bukaci al'ummar jihar suyi watsi da jita jitar cewa wasu 'yan bindiga za su kawo hari a birnin ta Kano.

Ya bayar da tabbacin cewa rundunar yan sandan da sauran hukumomin tsaro za su kasance cikin shiri domin magance duk wani barazanar tsaro da ka iya tasowa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Habu, wanda ya bayar da wannan tabacin yayin bikin karin girma da aka yi wa jami'an rundunar 252, ya amsa cewa sun sami wannan rahoton amma ya yi alkawarin samar da isashen tsaro don dakile duk wani abu da ka iya tasowa.

Ya kara da cewa 'Yan sanda da takwarorinta na tsaro sun bincika dukkan wuraren da ake zargin 'yan bindigan za su iya samun mafaka amma ya ce a yanzu babu wani dalilin da zai sa mutane su tayar da hankulansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel