IGP ya janye wasu jami'an rundunar 'yan sanda daga EFCC

IGP ya janye wasu jami'an rundunar 'yan sanda daga EFCC

Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya janye wasu manyan jami'an 'yan sanda da ke aiki tare da hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC).

Jaridar 'The Cable' ta rawaito cewa kiranyen na IGP Adamu zai shafi a kalla shugaban shiyya guda 20 a hukumar EFCC.

An saki dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, kamar yadda rahotannin yammacin ranar Laraba, 15 ga wata Yuli, 2020, suka wallafa.

Jaridar TheCable ta wallafa cewa ''duk da bayanan sharudan bayar da belin Magu sun yi wuyar samu, majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa ya koma gidansa."

An saki Magu bayan sati biyu da fara bincikensa bisa zarginsa da almundahana da kuma rashin biyayya, kamar yadda ministan shari'a, Abubakar Malami, ya rubuta korafi a kansa zuwa fadar shugaban kasa.

Tun bayan fara gurfanarsa a gaban kwamitin bincike da shugaban kasa ya kafa, Magu bai koma gida ba, ya na tsare a hedikwatar rundunar 'yan sanda ta kasa, kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.

Magu ya fara gurfana a gaban kwamiti bincike a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, kuma tun daga ranar wasu jami'an 'yan sanda su ka yi awon gaba da shi zuwa hedikwatarsu.

Jami'an 'yan sanda ne su ke kai Magu fadar shugaban kasa duk lokacin da zai bayyana a gaban kwamitin bincike domin cigaba da amsa tambayoyi a kan tuhume - tuhumen da ake yi masa.

IGP ya janye wasu jami'an rundunar 'yan sanda daga EFCC
IGP M. A. Adamu
Asali: Facebook

Babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu, ya sanar da Ibrahim Magu cewa ba shine keda alhakin tsarewar da aka yi masa ba.

Tosin Ojoamo, lauyan Magu, ya rubuta takardar neman belin Magu zuwa ofishin babban sifeton rundunar 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta gargadi kananan sojoji a kan yin aiki da 'zugar' su kashe shugabanninsu

Sai dai, a cikin wasikar martani mai lamba CB: 7000/IGP/.SEC/ABJ/VOL.489/171 da IGP ya aikawa lauyan Magu, ya sanar da shi cewa ya karkata akalar bukatarsa zuwa gaban kwamitin da ke binciken zarge - zargen da ake yi wa Magu.

IGP ya aikawa Ojoamo wasikar ne a ranar Talata, 14 ga watan Yuli, 2020, kwanaki hudu bayan lauyan ya aika wasikar neman belin Magu.

Wani bangare na wasikar ya bayyana cewa; "IGP yana son jan hankalinka a kan cewa rundunar 'yan sanda ba ta binciken C.P. Ibrahim Magu (mutumin da ka ke wakilta), kwamitin shugaban kasa da ke binciken harkokin hukumar EFCC ne ya ke bicikensa.

"A saboda haka, IGP yana shawartarka ka karkatar da bukatarka zuwa shugaban kwamitin bincike domin samun amsar da ta dace."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel