Abubuwa sun dagulewa Godwin Obaseki: Jerin mutane 42 da sukayi murabus daga gwamnatinsa
- Abubuwa na neman dagulewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki
- Ma'aikatansa da magoya bayansa na hannun riga da shi ana sauran yan makonni zaben gwamnan jihar
- Kawo yanzu mambobin kwamitin yakin neman zabensa akalla da abokan aikin sun yi murabus kuma sun koma bayan dan takaran APC
Abubuwa na neman rikicewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, yayinda manyan ma'aikata da abokan aikinsa suke fita daga gwamnatinsa ana sauran yan makonnin zabe.
Gwamnan ya fara fuskantar wannan kalubale ne tun bayan lokacin da ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress APC zuwa jam'iyyar People Democratic Party PDP.
Sakamakon fitarsa, wasu mabiyansa irin tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Kabiru Adjoto, sun bi sahunsa.
Amma da alamun wadanda suka fita daga tafiyarsa sun fi adadin wadanda suka bisa.

Asali: UGC
Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin sunayen mutane 42 da sukayi murabus daga gwamnatin Obaseki:
1. John Mayaki - Sakataren yada labarai
2. Kehinde Garrick Osemwingie - sakataren Uhumwonde LGC
3. Taiwo Akerele - Shugaban ma'aikatar fadar gwamnatin jihar
4. Paul Ohonbamu - Kwamishana
5. Maureen Osaro Ekhoragbon - Mataimakin shugaban karamar hukumar Ovia North East
6. Omua Oni-Okpako - Kwamishana
7. Fulani Yakubu Ekpeyoung -SSA
8. Hon. Adeyanju Noah - SSA
9. Madam Cordelia M. Iyogun - SSA
10. James Osheku - SSA
11.Louis Osamuyi Osayande - SSA
12. Ernest Unuaghon imina - SSA
13. Goodluck A. Uyigue - SA
14. Hon. Razaq Rotimi - SA
15. Olajide Victor Oloruyomi - SA
16. Smart Bank - SA
17. Chris Oseiwe Oribhabor - SSA
18. Comr. Solomon Okoduwa - SSA
19. Kennedy Itepu - SSA
20. Sabbath Egbeyon - SSA
21. Osamwonyi Atu - EDSOGPADEC
22. Emmanuel Odigie - EDSOGPADEC
23. Aiwanu Oshiomhole - EDSOGPADEC
24. Okondoh Patrick Iyoha - OSM State director
25. Gabriel Oiboh - Shugaban hukumar makarantun sakandare
26. Bright Njor - SA
27. Kingsley Ekueme - SA
28. Joshua Akhabue - SA
29. Oladele Ayotope Josiah - SA
30. Boyi Magdalene - SA
31. Osarobo Osaro Anthony - SA
32. Aibangbee Chico - SA
33. Obayagbona Augustine - SA
34. Otaniyen Igbinosa - Orhiomwon supervisor
35. Martins Ozakpolor - Orhiomwon supervisor
36. Vincent Ehibor - Orhiomwon supervisor
37. Christopher Adesotu - Shugaban hukumar ilmin aikin hannu
38. Festus Ese Omoruyi SA -
39. Aghedo Oscar - Sakatare Ovia North East
40. Emike Obazee - SA
41. Monday Ogiegor - MD EDSTMA
42. Prince Lucky Igbinedion - SSA
A bangare guda, tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, ya tabbatarwa mabiya jam'iyyar cewa zasu samu gagarumin nasara a zaben bana.
Za'a gudanar da zaben ne ranar Asaba, 19 ga watan Satumba, 2020.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng