Babbar Sallah: A fadar Villa zan yi Sallar Idin bana - Buhari

Babbar Sallah: A fadar Villa zan yi Sallar Idin bana - Buhari

Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi Sallar Idin bana a fadar Villa daga shi sai iyalansa a matsayin matakin dakile bazuwar cutar korona.

Babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu shi ne ya bayyana hakan a cikin wani sako da ya wallafa kan shafinsa na sada zumunta a ranar Laraba.

A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar, ya ce shugaba Buhari zai yi Sallar Idin bana tare da iyalinsa a gida kuma ba ya bukatar kowa ya kawo masa gaisuwar

Mallam Shehu ya ce hakan ya yi daidai da shawarari da kuma ka'idodin da mahukuntan lafiya suka shar'anta domin dakile yaduwar annobar korona.

Yayin da Buhari ya halarci Idin karamar Sallah a fadarsa
Hoto daga fadar shugaban kasa
Yayin da Buhari ya halarci Idin karamar Sallah a fadarsa Hoto daga fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

A karshe shugaban kasar yana taya daukacin al'ummar Najeriya murnar bikin Babbar Sallah ta bana da za a gudanar a ranar Juma'a, 31 ga watan Yuli, wanda ya yi daidai da 10 ga watan Zhul Hijja a kalandar Musulunci.

Ana iya tuna cewa, a karamar Sallah da ta wakana fiye da watanni biyu da suka gabata, shugaba Buhari ya yi Sallar Idi ne a gida tare da iyalansa.

KARANTA KUMA: Tambuwal ya dora alhakin kalubalen ta'addancin da ya addabi Najeriya a kan rashin hadin guiwa

Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa hakan biyayya ce ga umarnin Sarkin Musulmi; Alhaji Sa’ad Abubakar III, wanda ya bai wa daukacin al'ummar Musulmin Najeriya umarnin yin Sallar a gida tare da iyalansu.

Kafin bullar annobar korona, shugaba Buhari yana halartar Sallar Idi a cikin taron Jama'a a kowane daya daga cikin filayen Idi da ke birnin Abuja, idan har bai samu damar komawa mahaifarsa ta Daura da ke jihar Katsina ba.

Kuma bayan nan, mazauna Abuja ciki har da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, shugabannin addinai, ministoci, 'yan majalisar tarayya da sauransu, su kan kai masa ziyara har gida domin yi masa gaisuwa da taya shi murnar bikin Sallah.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel