Barazanar harin 'Yan Bindiga a Kano: Rundunar Yan sanda ta yi ƙarin haske

Barazanar harin 'Yan Bindiga a Kano: Rundunar Yan sanda ta yi ƙarin haske

Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Kano, Mr Habu A. Sani a ranar Talata ya bukaci al'ummar jihar suyi watsi da jita jitar cewa wasu 'yan bindiga za su kawo hari a birnin ta Kano.

Ya bayar da tabbacin cewa rundunar yan sandan da sauran hukumomin tsaro za su kasance cikin shiri domin magance duk wani barazanar tsaro da ka iya tasowa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Habu, wanda ya bayar da wannan tabacin yayin bikin karin girma da aka yi wa jami'an rundunar 252, ya amsa cewa sun sami wannan rahoton amma ya yi alkawarin samar da isashen tsaro don dakile duk wani abu da ka iya tasowa.

Barazanar harin 'Yan Bindiga a Kano: Rundunar Yan sanda ta yi karin haske
Kwamishinan Yan sandan Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Ya kara da cewa 'Yan sanda da takwarorinta na tsaro sun bincika dukkan wuraren da ake zargin 'yan bindigan za su iya samun mafaka amma ya ce a yanzu babu wani dalilin da zai sa mutane su tayar da hankulansu.

DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba

Kwamishinan na 'Yan sanda ya yi kira ga al'ummar musulmi su gudanar da bukukuwar sallarsu cikin zaman lafiya ta kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Ya bukaci mazauna Kano su cigaba da harkokinsu da kasuwanci kamar yadda suka saba amma ya ce su yi gaggawar kai rahoton duk wani mutum ko mutane da ba su gamsu da su ba don taimakawa 'yan sanda kawar da bata gari.

CP Sani ya yi kira ga jamian da aka yi wa karin girman su cigaba da jajircewa da gudanar da aikinsu cikin gaskiya da rikon amanar da rundunar ta damka a hannunsu.

Wadanda aka yi wa karin girman sun hada da Mataimakan Sufritandan 'Yan sanda, (DSP) guda tara da aka yi wa karin girma zuwa Sufritandan Yan sanda (SP).

Sai kuma (ASP) guda hudu da aka yi wa karin girma zuwa DSP da kuma Sufeta guda 239 da aka yi wa karin girma zuwa ASP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel