Yanzu Yanzu: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa karo na 10 ta yanar gizo

Yanzu Yanzu: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa karo na 10 ta yanar gizo

- A karo goma ta yanar gizo, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

- An fara taron da karfe 10:00 na safe inda aka yi shiru na minti guda domin karrama mahaifin gwamnan jihar Kwara, Abdulganiyu Abdulrazak (SAN) wanda ya rasu

- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da wasu ministoci da manyan jami'an gwamnati sun hallara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa karo na goma ta yanar gizo a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Taron, wanda aka fara da misalin karfe 10:00 na safe da rera taken kasa, ya kuma hada da yin shiru na minti guda domin karrama mahaifin gwamnan jihar Kwara, Abdulganiyu Abdulrazak (SAN), wanda ya kasance ministan sufurin jirgin kasa a jumhuriya ta farko.

Taron na yanar gizo ya kuma samu halartan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Ciki harda shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da kuma babban mai ba kasa shawara a kan tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno.

Yanzu Yanzu: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa karo na 10 ta yanar gizo
Yanzu Yanzu: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa karo na 10 ta yanar gizo Hoto: Nairametrics
Asali: UGC

Ministocin da suka hallara da kansu sun hada da Atoni-janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami; minister kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Misis Zainab Ahmed.

Sauran sune; ministan sufuri, Sanata Hadi Sirika; ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola; ministan muhalli, Mohammed Mahmoud, ministan kasuwanci, Niyi Adebayo.

KU KARANTA KUMA: Rikicin kudancin Kaduna: Rashin isassun ma'aikata ke mayar mana da aiki baya - Rundunar soji

Har ila yau wadanda suka hallara ido da ido harda ministan wutar lantarki, Injiniya Saleh Man da ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed.

Sauran ministocin sun shiga taron ne daga ofishoshinsu mabanbanta da ke Abuja,jaridar The Nation ta ruwaito.

A wani labarin kuma, gwamnonin jam'iyyar APC sun ce suna farin ciki da salon shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A taron da suka yi da shugaban kasar ta yanar gizo a ranar Talata, gwamnonin sun ce shugaban kasar ya shawo kan matsalolin tsaro da na tattalin arziki.

Sun bayyana yadda ya fitar da kasar daga halin rushewar tattalin arziki a 2016 da kuma annobar Coronavirus a matsayin wasu daga cikin nasarorin shugaban kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel