Cikin mako daya, an kashe mutane 142, an yi garkuwa da 44 a Arewacin Najeriya

Cikin mako daya, an kashe mutane 142, an yi garkuwa da 44 a Arewacin Najeriya

Akalla mutane 142 aka kashe a hare-hare daban-daban a Arewacin Najeriya cikin mako daya (18 ga Yuli zuwa 24 ga Yuli), wani rahoton da Premium Times ta samu ya nuna.

Hakazalika an yi garkuwa da mutane akalla 44 a Arewa yayinda matsalan rashin tsaro ke cigaba munana a fadin tarayya.

A cewar rahoton cibiyar harkokin waje CFR, adadin wadanda suka mutu sun fi yawa a jihar Kaduna sakamakon hare-hare shida da akai, sannan jihar Katsina, mahaifar shugaba Muhammadu Buhari, inda aka kai hare-hare hudu.

Cibiyar ta kasar Amurka, ta ce tana bibiyan matsalan rashin tsaro a fadin Najeriya "ta hanyar amfani da labaran da aka wallafa a jaridu, kuma daga iyalan wadanda aka kaiwa hare-hare."

Cikin mako daya, an kashe mutane 142, an yi garkuwa da 44 a Arewacin Najeriya
Cikin mako daya, an kashe mutane 142, an yi garkuwa da 44 a Arewacin Najeriya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Na fi karfin inyi fada a Dogara, ya yi kadan - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed

Filla-filla:

A bayanan filla-filla, rahoton ya bayyana cewa a ranar 23 ga Yuli, wasu makiyaya sun hallaka mutane bakwai a Kajuru, jihar Kaduna kuma washe gari ranar 24 ga Yuli, yan bindiga sun hallaka mutane 10 a karamar hukumar Jema'a da Kaduna, duk a jihar Kaduna.

A ranar 18 ga Yuli, an yi garkuwa da mutane shida a Chikun, jihar Kaduna, yayinda ake zargin makiyaya da kisa mutane 11 a Zangon Kataf ranar 20 ga Yuli.

Rahoton ya kara da cewa a ranar 19 ga Yuli, wasu makiyaya sun hallaka mutane 21 da wani dan sanda a Kaura, yayinda rikici kabilanci yayi sanadiyar mutuwar mutane uku a Kauru, jihar Kaduna ranar 21 ga Yuli.

A cewar rahoton CFR, bam ya hallaka yara shiga a Malumfashi, jihar Katsina ranar 18 ga Yuli, yayinda aka hallaka Sojoji 23 da yan bindiga 17 a Jibia, jihar Katsina.

Washe gari ranar 21 ga Yuli, yan bindiga sun hallaka mutane uku a Batsari yayinda aka sace mutane 17 a Safana ranar 22 ga Yuli a jihar Katsina.

A cewar rahoton, yan Boko Haram sun kashe ma'aikatan kungiyoyin agaji biyar a ranar 22. Kuma a ranar sun hallaka mutane uku a garin Chibok.

A ranar 20 ga Yuli, harin jirgin saman Soji yayi sanadiyar mutuwar akalla yan bindiga 10 a Talata-Mafara, jihar Zamfara, yayinda aka sake hallaka yan bindiga 10 a hanyar Birnin Magaji/Kiyawa na jihar ranar 23 ga Yuli.

A jihar Tarana ranar 19 ga Yuli, masu garkuwa da mutane sun kashe mutane biyu da suka sace yayinda jami'an tsaro suka hallaka masu garkuwa hudu a hanyar Lokoja, jihar Kogi a ranar.

Rahoton ya karashe cewa a ranar 19 ga Yuli, an yi garkuwa da mutane 16 a Rafi, jihar Neja, yayinda akayi garkuwa da mutane 5 a Jada, jihar Adamawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel