Na fi karfin inyi fada da Dogara, ya yi kadan - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed

Na fi karfin inyi fada da Dogara, ya yi kadan - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed

Gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed, ya siffanta tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da ya sauya sheka zuwa All Progressives Congress APC a matsayin annoba a siyasa.

Ya zargi Dogara da kara kudi a kwangila a ayyukan da yakeyi a mazabarsa.

Ya bayyana hakan ne yayinda daruruwan masoya daga kananan hukumomin Dass, Tafawa Balewa da Bogoro, da Yakubu Dogara ke wakilta suka kai masa ziyara gidan gwamnati ranar Talata.

Yace, "Bayan karamar hukumar Bauchi, babu inda na samu dimbin kuri'u kaman Dass, Tafawa Balewa da Bogoro kuma ko a shekarun baya na samu wadannan kuri'u lokacin da nike ANPP; kuri'un da na samu lokaci sun ninka na Dogara sau 20."

"Yanzu da nayi takaran zaben gwamna, kuri'un da na samu sun fi nashi kuma saboda haka, duk abinda zan yi muku, ba dan Dogara zan yi ba, zan yi ne saboda Allah kuma saboda kai na."

"Wadannan karerayin da yake kaina, ya ce bamu baiwa kananan hukumomi kudi, amma haka kananan hukumomin suke a da? Shin baku ganin abubuwan da mukeyi?

"Kawai yana zuba ne saboda idan ka ga kare na gudu, imma yana kokarin cimma wani abu ne ko wani abu na bin shi. Muna tausayinshi saboda ya zama annoba a siyasa, amma a idonmu 'yan uwa da dattawa, ya zama abin kunya."

Gwamnan ya ce ba zai iya fada da Dogara ba saboda "shi (Dogara) ya yi karami; wadanda suka fi shi ma sun yunkura kuma sun fadi."

Na fi karfin inyi fada da Dogara, ya yi kadan - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed
Na fi karfin inyi fada da Dogara, ya yi kadan - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed
Asali: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa, Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya musanta dukkan zargin rashawa da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya kwatanta shi da su.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin da ya karba bakuncin 'yan majalisa masu wakiltar mazabar Dass/Tafawa Balewa/Bagoro a Bauchi.

Dogara na wakiltar mazabar ne a majalisar wakilai.

Tsohon kakakin majalisar wakilan ya zargi Gwamna Bala Mohammed da waskar da bashin N4.5 biliyan da ya karbo, kara kudin kwangila da watanda da kudaden karamar hukuma a matsayin dalilan da yasa ya bar PDP tare da komawa APC.

"Abun takaici ne kuma mara dadi saboda matashi ne da muke matukar kauna, har da ni. Ko a yanzu, ban rike shi da komai ba," Mohammed yace.

Ya kara da cewa, "Amma ya zo ya nuna mana asalin kalarsa, ya hada mana karya, wacce ta bashi damar hada kai da ni kuma ya yi nasarar komawa kujerarsa bayan hannun riga da suka yi da tsohon gwamna."

Asali: Legit.ng

Online view pixel