Abubuwa 5 da ya kamata a sani game da falalar ranar Arfa

Abubuwa 5 da ya kamata a sani game da falalar ranar Arfa

Ranar 9 ga watan Zul-Hijjah na duk shekarar Hijira ita ce ranar Arfa. A wannan ranar ne Alhazai ke taruwa a filin Arfa da ke cikin garin Makkah.

Suna fara taruwa ne bayan kaucewar rana daga tsakiyar sama zuwa lokacin da za ta fadi don aiwatar da daya daga cikin rukunan aiki Hajji.

BBC Hausa ta tattauna da shahararren malamin addinin Musulunci, Dr Ibrahim Disina, a kan abubuwan da suka kamata Musulmi ya yi a wannan ranar mai albarka.

Abubuwa biyar cikin falalar wannan rana sun hada da:

1. A ranar Arfar Hajjin ban kwana na zamanin Annabi Muhammad, Allah ya cika addinin Musulunci. Abin nufi, tun daga ranar ba a sake saukar da wasu hukunce-hukunce na addini ba.

Hakan ne yasa sayyidina Umar Radiyallahu anhu ya ce: "Saboda muhimmancin wannan ranar, da Yahudawa ne, ba shakka za su dauketa ranar biki na kowacce shekara".

Hakazalika, bayan kwanki 81 da wannan ranar, Allah ya karba rayuwar shugabanmu, Annabi Muhammadu (S. A. W).

2. Abu mafi tsada da daraja a cikin duk addu'o'i da za a yi a duniya shine yin addu'a yayin tsayuwar arfa, fadin Annabi Muhammadu ne hakan.

"Mafificiyar addu'a ita ce addu'ar ranar Arfa," cewar Annabi Muhammadu S. A. W.

Abubuwa 5 da ya kamata a sani game da ranar arfa
Abubuwa 5 da ya kamata a sani game da ranar arfa. Hoto daga BBC Hausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon rikici ya barke a APC: Wasu 'ya'yan jam'iyyar na yunkurin sauya sheka, sun bada dalili

3. A ranar Arfa ne Allah madaukakin Sarki ke yawaita 'yanta bayinsa daga shiga wutarsa.

Wannan ya zo a cikin abin da Imam Muslim ya ruwaito. Ya ce, "Annabi ya ce babu wata rana da Allah ke yawaita 'yanta bayinsa daga shiga wutarsa kamar ranar Arfa."

4. Azumtar ranar Arfa na kankare zunubban shekaru biyu kamar yadda ya zo daga Annabi Muhammadu S. A. W.

Mai tsira da amincin Allah ya ce, "Azumtar ranar Arfa na kankare zunubban shekarar da ta gabata da ta mai zuwa," Muslim ya ruwaito.

5. Allah madaukakin sarki yana alfahari da Hujjaj da suka halarci wannan yinin.

Imam Ahmad ya ruwaito cewa: "Mai tsira da amincin Allah ya ce, "Allah yana Alfahari da mazauna sama da wadanda suka halarci filin Arfa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel