Kisan uwar dakinta: Kotu ta yankewa mai aiki hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kisan uwar dakinta: Kotu ta yankewa mai aiki hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Wata babbar kotu da ke zama a garin Fatakwal ta yankewa wata mai aiki mai suna Telema Amosu hukuncin kisa

- Kotun ta kama Amaso da laifin kashe uwar dakinta mai suna Helen Ibiba Bobmanuel a watan Satumban 2013

- Baya ga haka, ta taimakawa wani mai suna Chukwuemeka wurin satar mota, waya da na'ura mai kwakwalwa duk mallakin marigayiyar

Wata babbar kotu da ke zama a Fatakwal ta yankewa wata Telema Amaso hukuncin kisan ta hanyar rataya, sakamakon kisan marigayiya Helen Ibiba Bobmanuel da tayi a 2013.

An kama ta da laifin shake uwar dakinta a gidanta da ke yankin Woji na jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Amaso, wacce aka kama da laifin kisan kai, hadimar marigayiya Bobmanuel ce da marigayin mijinta a lokacin da ta aikata laifin.

Mai laifin tare da wani Ndubuisi Chukwuemeka sun gurfana ne a kan laifin hada kai wurin kisan kai da kuma sata amma an soke zargin hada kai wurin kisan kai.

Kisan uwar dakinta: Kotu ta yankewa mai aiki hukuncin kisa ta hanyar rataya
Kisan uwar dakinta: Kotu ta yankewa mai aiki hukuncin kisa ta hanyar rataya. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Sabon rikici ya barke a APC: Wasu 'ya'yan jam'iyyar na yunkurin sauya sheka, sun bada dalili

A yayin yanke hukuncin a ranar Talata, Mai shari'a Silverline Irangonima, ya ce masu kare kansu na farko da na biyun an kama su da laifi, saboda shaidu gamsassaun da aka mika gaban kotu wanda ya hada da amsa laifinsu da suka yi a gaban 'yan sanda.

Mai Shari'a Irangonima ya ce, duk da mai kare kanta ta farko, Amaso, ta musanta tare da janye amsa laifinta da tayi a gaban 'yan sanda, ba a samu gamsassun shaidu da suka tabbatar da hakan ba.

A yanke hukuncin wanda ake tuhuma na biyu a kan sata, Chukwuemeka, Mai shari'a ya ce kotun ta kama shi da laifin saboda ikirarinsa bai gamsar da kotun ba da har za ta wanke shi da laifin.

An kama mutum biyu a ranar 17 ga watan Satumban 2013, jim kadan bayan samun gawar Bobmanuel.

An kuma tarar da cewa kadarorinta masu darajar N5 miliyan, wanda suka hada da mota, waya da na'ura mai kwakwalwa duk mai aikin ta kwashesu tare da hadin bakin Chukwuemeka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel