Zargin rashawa: Gwamnan Bauchi ya zargi Dogara da yi masa sharri

Zargin rashawa: Gwamnan Bauchi ya zargi Dogara da yi masa sharri

Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya musanta dukkan zargin rashawa da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya kwatanta shi da su.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin da ya karba bakuncin 'yan majalisa masu wakiltar mazabar Dass/Tafawa Balewa/Bagoro a Bauchi.

Dogara na wakiltar mazabar ne a majalisar wakilai, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Tsohon kakakin majalisar wakilan ya zargi Gwamna Bala Mohammed da waskar da bashin N4.5 biliyan da ya karbo, kara kudin kwangila da watanda da kudaden karamar hukuma a matsayin dalilan da yasa ya bar PDP tare da komawa APC.

"Abun takaici ne kuma mara dadi saboda matashi ne da muke matukar kauna, har da ni. Ko a yanzu, ban rike shi da komai ba," Mohammed yace.

Ya kara da cewa, "Amma ya zo ya nuna mana asalin kalarsa, ya hada mana karya, wacce ta bashi damar hada kai da ni kuma ya yi nasarar komawa kujerarsa bayan hannun riga da suka yi da tsohon gwamna."

Gwamnan ya tabbatar wa da sauran shugabannin PDP a Najeriya cewa Bauchi na nan tasu ce.

Zargin rashawa: Gwamnan Bauchi ya zargi Dogara da yi masa sharri
Zargin rashawa: Gwamnan Bauchi ya zargi Dogara da yi masa sharri. Hoto daga Channels TV
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sabon rikici ya barke a APC: Wasu 'ya'yan jam'iyyar na yunkurin sauya sheka, sun bada dalili

A wani labari na daban, Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, wanda ya dawo jam’iyyar Progressives Congress (APC) bai aikata kowani laifi ba kamar yadda hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bayyana.

A cewarsa, tsohon kakakin majalisar bai take doka ba a wannan hukunci da ya yanke.

Ya wallafa a shafinsa na twitter cewa: "Wannan shine ainahin siyasa, ba a karya kowani doka ba a nan, Obaseki ya tafi kuma dogara ya dawo. Wannan shine tsarin wannan wasar, idan ka tafi, wani zai dawo ya cike gurbin.

"Kuma zai ci gaba a haka har zuwa karshen wasan. abu mafi ahla, kada ka damu kanka a kai. Ka kasance a tsaka-tsaki."

Ku tuna cewa Dogara ya bar APC zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da tsohon Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da wasu gwamnoni gabannin zaben 2019.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel