Gwamnan Plateau ya haramta Sallar Idi saboda korona

Gwamnan Plateau ya haramta Sallar Idi saboda korona

Gwamnatin Jihar Plateau ta haramta Sallar Idi a jihar a bana yayin da adadin mutanen da suka kamu da cutar a jihar ta kai 982.

Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 na jihar, Gwamna Simon Lalong ne ya sanar da haramcin yayin jawabin da ya yi wa manema labarai kan matakan da jihar ke dauka kan annobar a ranar Talata a Jos.

Gwamnan ya kuma haramta duk wasu bukukuwa da aka saba yi da sallah da suka hada da ziyartar wuraren shakatawa da gidajen dabobin namun daji da sauransu.

Gwamnan Plateau ta haramta Sallar Idi saboda korona
Gwamnan Plateau ta haramta Sallar Idi saboda korona. Hoto daga Premium Times
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi

"Dukkan mazauna jihar suyi amfani da takunkumin fuska, musamman yara a lokacin da suke kai wa yan uwa da abokan arziki abinci," in ji shi.

Mr Lalong ya ce hakan ya zama dole ne bayan karuwar adadin masu cutar da aka samu a jihar tare da bikin sallar da ke karatawo domin dakile yaduwar cutar.

Gwamnatin tarayya dai ta sanar da ranakun Alhamis da Jumaa a matsayin ranakun hutu domin musulmi su yi bikin sallar babba.

Gwamnan wanda ya samu sakataren gwamnatin jihar, Danladi Atu, ya wakilta ya shawarci dattawa su zauna a gida duba da cewa su suka fi rauni idan cuta ta kama su.

Mr Lalong ya kuma tunatar da mazauna jihar game da dokar takaita fita da gwamnatin tarayya ta saka na karfe 4 na asuba zuwa 10 na dare tana nan tana aiki.

Ya ce an samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar a jihar saboda akwai dakin gwaje gwaje guda uku a jihar: Cibiyar Binciken Dabobbi ta Kasa da ke Vom; Asibitin Kwararru da ke Plateau da Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Plateau.

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Sarkin Musulimi Sa'ad Abubakar ya bukaci hakimai da shugabannin addini suyi limancin sallar Idi a masallatan Juma'a a maimakon zuwa filayen sallar Idi.

Sultan din ya bayar da wannan shawarar ce yayin da ya ke sanar da cewa a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2020 ce ranar babbar Sallah kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

A cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba 22 ga watan Yuli, Sultan Abubakar ya yi kira ga alummar musulmi suyi adduo'in zaman lafiya da samun cigaba a kasar.

"Mai alfarma, Alhaji Muhammad Saad Abubakar CFR, mni, Sultan din Sokoto kuma shugaban Kwamitin Koli ta Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ya sanar da cewa ranar Juma'a 31 ga watan Yulin 2020 da ya yi daidai da ranar 10 ga watan Zulhijja ta 1441 AH ne za ayi babbar sallar wannan shekarar," in ji sanarwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel